Ayyukan da za su ɓace da waɗanda za su haɓɓaka a nan gaba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Oleg Karpyak
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Ukrainian
- Lokacin karatu: Minti 8
Fannin ayyukan gwamnati na sauyawa cikin sauri, kuma da alama da dama daga cikin ayyukan da ake yi yanzu, nan gaba kaɗan za su iya gushewa.
Wani bincike da cibiyar World Economic Forum (WEF), ta gudanar a baya-bayan nan, ya nuna cewa abubuwa biyu ne za su haifar da sauyin: Ɓullowar sabbin fasahohi da yadda na'urori ke aiki da kansu da kuma komawa amfani da masana'antu marasa gurɓata muhalli da ɗorewar hakan.
Ana hasashen cewa saurin bunƙasar fannonin fasahar zamani kamar sarrafa manyan bayanai, da komawa amfani da komfutoci da kuma ƙirƙirarriyar basira na daga cikin abubuwan da ke haddasa sauye-sauyen a fannonin aiki.
Labari mai daɗi shi ne zuwan sabbin fasahohin zamanin, zai taiamaka matuƙa wajen bunƙasa fannin tattalin arziki, domin kuwa yayin da hakan zai rage ayyukan yi, a gefe guda kuma zai samar da wasu. Baya ga hakan idan kasuwanci ya samu riba mai yawa ta hanyar zuba jari ƙalilan, hakan na nuna ɓunƙasar kasuwancin da cin riba mai yawa.
Masu bincike daga cibiyar WEF, sun ce kusan kashi ɗaya bisa huɗu na ayyukan da ake yi yanzu za su sauya cikin shekara biyar masu zuwa.
Don haka, idan mutum na buƙatar samun nasara da gurbin aiki a sabbin fannonin da ke tafe, dole ne ya samu ƙwarewa da koyon sabbin abubuwa.
Babbar ƙwarewar da ake buƙata
Ilimin fasahar zamani: Wannan shi ne ginshiƙi abin da mutum zai koya domin samun damar fafatawa don samun gurbin aiki a sabbin fannnin ayyukan yi .
Hakan ba yana nufin dole sai kowa ya koyi harsunan da kwamfuta ke aiki da su ba ko ya fahimci yadda na'urori ke gudanar da duka ayyukansu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma a nan gaba, an yi amanna cewa ayyukan STEM za su zama ayyukan da aka fi buƙata a nan gaba.
'STEM' kalma ce da ake amfani da ita wajen dunkule ayyuka mabambanta, amma masu alaƙa da juna a fannonin kimiyya da fasaha da injiniyanci da kuma lissafi.
Don haka idan kana tababa kan darasin da ya kamata 'ya'yanka su mayar da hanakali a kai a makaranta, ga amsarka a nan: Lissafi da ilimin Komfuta da kuma yadda abubuwa ke aiki a duniya, wato 'Natural Sciences.
Tunani mai zurfi: Abu na gaba shi ne tunanin warware matsaloli. Domin bunƙasa wannan fanni ana buƙatar mutum ya inganta ƙaifin ƙwaƙwalwarsa, ta yadda zai iya fahimtar matsala, da yadda zai warware ta don samar da mafita da ba ta da wasu matsaloli a tattare da ita.
Domin samun damar hakan, kana buƙatar samun horon yadda za ka saurari abubuwa cikin nutsuwa da mayar da hankali, saboda sabbin na'urori da shafukan sada zumunta da wasannin yanar gizo da sauran tallace-tallace kan janye hankalin mutane daga mayar da hankail don koyon sabbin abubuwa.
Ƙwarewa a zuzzurfan tunani ya haɗa da ƙoƙarin gano abubuwa da ci gaba da ilimantar da kai da kuma ci gaba da ingantuwar koyo, don haka kana buƙatar mayar da hankali do cimma wannan.
Koyon Turanci zuwa maƙura na da matuƙar muhimmancin da ya kamata a samu.
Haka kuma, ƙirƙirar sabbin abubuwa a fannonin kimiyya da injiniyanci da zane-zane, na da matuƙar mihimmanci idan aka gwama su da ilimin fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire.

Asalin hoton, Getty Images
Sadarwa ko fahimtar mutane: Waɗannan manyan abubuwa ne guda biyu da ya kama mutum ya san su, musamman a wannan lokaci na ƙirƙirarriyar basira.
Duk da yadda ake samun saurin bunƙasar na'urori, koyaushe ana buƙatar mutane domin yin wasu abubuwan, don haka ana buƙatar taimakon ɗa'adam, da aiki tare da sauraron mutane da bayar da labari, da tallafa wa da kuma fahimtar halin da wasu ke ciki zai taimaka matuƙa.
Wani rahoto da aka wallafa a 2020 a manhajar LinkedIn, a fannin shafukan sada zumunta, ƙwarewar sadarwar ta zama abin da aka fi buƙata a fanni ya zuwa yanzu.
''Yayin da ake ci gaba da amfani da fasahar ƙirƙrirariyar basira da mutum-mutumi a wuraren ayyuka, da ƙaruwar aiki a wuraren aikin , kuma fasahar zamani za ta ba mu damar haɗa mutane da ke faɗin duniya domin su yi aiki tare, abu mafi muhimmanci shi ne ayyada za mu yi magana don fuskantar juna domin samar da wannan damar,'' in ji Dan Negroni, wani ƙwararre a fannin kwadago.
Sabbin fasahohi
Babau mamaki, idan sabbin fasahohin zamani da kimiyya da fasaha su kasance cikin fannonin da za su fi samun bunƙasa a nan gaba. Bunƙasar fannin ƙirƙirarriyar basira da koyon abubuwa da na'urori za su kawo ɓullowar damarmaki a fannin.
Ɗaya daga cikin manayn damarmakin da za a a samu a nan shi ne injiniyan AI, wanda zai riƙa isar da saƙo ga AI, ya kuma taimaka wajen daidai saƙon da ake buƙatar tura wa AI, zai kasance ƙwararren tafinta tsakanin mutane da kuma AI.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƙarin ayyuka da ke da alaƙa da AI sun haɗa da ƙwararrun masana ƙa'idoji, su ne masu ƙwarewa a fannin sanin ƙa'idoji, kuma injiniyoyin tsaron bayanai a intanet sannan kuma su ne masu masu ƙirƙirar manhajar tattaunawa tsakanin mutane da na'urori.
A taƙaice dai ana shawartar mutane da ke fargabar AI zai zame musu barazana a ayyukansu, su ɗauke shi a matsatin abokan aiki, saɓanin kishiya, sannan kuma su yi ƙoƙarin gano yadda za su yi aiki da shi.
Haka kuma wani babban fanni da za a samu damarmaki a cikinsa na gaba shi ne yadda ake sarrafa manyan bayanai, shi ne yadda za a sarrafa manyan bayanai daga manhajojin intanet irin su Netflix.
Haka kuma za a samu ƙarin damarmaki a fannin tsaron bayanai a intanet, saboda akwai yiwuwar samun ƙarin bayanai masu matuƙar muhimmanci a shafukan intanet.
Haka kuma za a samu ƙarin buƙatar masana fasahar kuɗi da masu sharhin kasuwanci da masu ƙirƙirar tsarin kuɗin intanet.
Ayyuka a masana'antu marasa gurɓata muhalli
Wani rahoto daga cibiyar Tattalin Arziki ta Duniya, WEF na 2023, ya nuna cewa za samu ƙarin ayyukan yi a fannin aiki da masana'atu marasa gurbata muhallai.
“Zuwa 2023, komawa amfani da masana'antu marasa gurɓata muhalli, a faɗin duniya, zai samar da ayyukan yi kimanin miliyan 30, a fannin manya da ƙananan fasahohi'', in ji rahoton.
A yanzu haka ƙasashen da ke samar da ayyukan yi a masana'antu marasa gurɓata muhalli a duniya da suka haɗa da ƙasashen Yamma da Japan da China na ci gaba da ƙaruwa.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗannan ayyukan suna da alaƙa da kasuwanci da kimiyya da siyasa ko kai-tsaye ga muhalli, tsakanin fannonin da ke aiki, don bunƙasa fannin makamashi marar gurɓata muhalli ko sabon makamashi da batura da adana na'urori da sauransu.
Haka kuma za a samu ƙaruwar buƙatar masu tsara birane, da masu tsare gine-gine da masu tsara taswira, da masu tsara fitattun gidaje na zamani.
Fannin lafiya
Yawan al'ummar duniya na ci gaba da ƙaruwa, kuma adadain shekarun da mutane ke rayuwa a duniya sun ƙaru, don haka dole a buƙaci ƙarin masu kula da mutane.

Asalin hoton, Getty Images
Don haka ƙwararru a fanin lafiya na daga cikin mutanen da za a fi buƙata a nan gaba.
Musamman likitoci masu muhammanci, waɗanda ba maganai kawai za su bai wa maras lafiya ba, har ma da taimakon inganta tarbiyya.
Don haka likitoci da sauran ƙwararru a fannin lafiya na buƙatar inganta ayyukansu ta hanyar koyon sabbin dabarun magance ciwo, musamman ta hanyar fasahar AI.
Sannan kuma da fannin kula da masu lalurar taɓin hankali da kuma sauran fannonin lafiya.
Ƙwarewar ayyukan hannu
Ƙwarewar ayyukan hannu, kamar masu gyaran na'urori da makanikai da masu gyaran wuta da masu haɗa wuta, na daga cikin ayyukan da za a ci gaba da buƙatarsu cikin shekaru masu zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
A wurare irin gyara da kanikanci da sauran ƙananna ayyuka doe ne a buƙaci ayyukan ɗan'adam.
To sai dai ana buƙatar su ƙara inganta ayyukansu ta hanyar amfani da fasahohin zamani, da amfani da sabbin kayan aiki, matsawar suna buƙatar duiya ta ci gaba da damawa da su.
Haka kuma ana a ran samun ƙaruwar buƙatar ayyuka a fannin noma. Al'ummar duniya na ci gaba da ƙaruwa, kuma dole kowa na buƙatar cin abinci. To amma za a fi buƙatar samun ƙwararrun injiniyoyin noma, maimakon manoman.
Ayyukan da ba za su jima a duniya ba
Akwai ayyuka da dama da nan gaba kadan za su ɓace a doron duniya. Irin waɗanna su ne ayyuka masu sauƙi ga injunan da ke aiki da kansu.
Ga jerin wasu ayyukan za su iya ɓacewa nan ba da jimawa ba:
- Mai kula da kwastomomi (masu biyan kudi, masu sayar da kaya, masu bayar da shawara, da sauransu);
- Masu kula da ofis (Saboda ƙaruwar aiki daga gida);
- Masu shigar da bayanai (Msu shigar da bayanai a fannin ƙididdiga, da kudi da masu rubuta bayanai, da masu fasasra bayanai)
- Masu ƙididdige alƙaluma;
- Ma'aikatan kamfanoni masu aiki mai guda a koyaushe.
Bayar da labari
Wani muhimmin fanni, da ba a fiya ambatar makomarsa a gaba ba, kuma da yiwuwar dole za a tafi da shi a nan gaban, shi ne bayar da labari.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar yadda dubban shekarun da suka gabata aka buƙaci fanni, haka fannin zai ci gaba da taka rawa a nan gaba.
Marubuta, da mawaƙa, da daraktoci da taurarin fina-finan da masu wasan barkwanci da masu kiɗe-kiɗe da mawaƙa, za su ci gaba da jan zarensu, duk kuwa da irin ƙalubalen da AI zai kawo musu.











