Ganduje ko Barau: Yadda rikicin nuna ƙwanji ya turnuƙe APC a Kano

Asalin hoton, Barau Jibrin/Facebook
Al'amuran siyasa na ɗaukar wani sabon salo a jam'iyyar APC ta jihar Kano tsakanin ɓangaren tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin.
Batun da ya ƙara fito da wagegiyar ɓarakar da ɓangarorin biyu suka daɗe suna ɓoyewa, ta fito fili ita ce takaddamar baya-bayan nan da ta kaure a jam'iyyar game da ayyana wanda zai yi wa jam'iyyar takarar gwamna a zaɓen 2027.
Da ma dai jim kaɗan bayan saukar Abdullahi Ganduje daga kujerar shugabancin APC, wasu ƴaƴan jam'iyyar suka fito suna neman shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas wanda na hannun daman Ganduje ne, ya sauka daga muƙaminsa shi ma.
Bugu da ƙari, a watan Agustan da ya gabata ma an yi wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC a Kano, inda ba a ga Sanata Barau Jibrin da ƙaramin ministan gidaje Abdullahi Ata ba.
Masu fashin baƙin siyasa na yi wa al'amarin kallon cewa rikici ne da zai iya yi wa jam'iyyar illa a nan gaba.
Ayyana Barau a matsayin ɗan takarar gwamna
Tun da farko dai wani ɓangare na tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jam'iyyar ta APC a Kano ne ya amince da cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin shi ne zai yi takarar gwamnan jihar a 2027.
Hon Muhammad Baffa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Takai shi ne ya jagorancin wasu tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin Kano 26 daga cikin 44 zuwa wurin mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibrin.
Ya ce babban dalilin da ya sa suka ɗauki wannan mataki shi ne bisa la'kari da yadda mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kwashe dogon lokaci yana ɗawainiya da jam'iyyar a jihar.
To amma jim kaɗan da bayyana hakan sai wani ɓangare ya fito yana cewa matsayar da aka cimma ba da yawunsa ba.
A wata sanarwa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sumaila, Ibrahim Hamisu ya fitar, ɓangaren da ya ce bai amince da hakan ba.
'Muna jaddada biyayya ga Ganduje'

Asalin hoton, Hon Kabiru Abubakar/Facebook
A wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC da ake gani ɓangaren Abdullahi Umar Ganduje ne ranar Alhamis, an cimma cewa lokaci bai yi ba na ayyana wani a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano.
Taron wanda aka yi a ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar mazaɓar Ghari/Tsanyawa, Injiniya Sani Bala ya kuma sake jaddada biyayyarsa ga tsohon shugaban jam'iyyar ta APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Mahalarta taron sun kuma ce suna sauraron umarnin Abdullahi Ganduje ne a matsayinsa na jagoransu a jihar domin "shi ne zai faɗi inda za a saka gaba."
Wa ke da ƙarfin faɗa a ji?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Kabiru Sufi wanda malami ne a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano kuma masanin kimiyyar siyasa, ya ce bisa tsarin siyasa, ana ganin mutumin da yake da wani babban muƙami fiye da duk wani ɗan jam'iyya kamar gwamna ko minista shi ne ya kamata ya zama jagora na jam'iyya a jiha.
"Abin da ya faru shi ne lokacin da Dr Abdullahi Ganduje ya sauka daga muƙamin gwamna an samu ɗan tsaiko kafin ya zama shugaban jam'iyyar APC, kuma a lokacin shi Sanata Barau Jibrin ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Saboda haka wannan abu ya sa aka samu rabuwar kai a tsakanin ƴan jam'iyyar inda wasu ke ganin shi Barau Jibrin ne ya kamata ya jagoranci jam'iyya," in ji Dakta Kabiru Sufi.
Sai dai Malam Kabiru Sufi ya ƙara da cewa a yanzu haka za a iya cewa mutanen biyu duk da babu alamar rabuwar kai a tsakaninsu a fili, amma kowa ya ja ɓangare guda kuma da jama'arsa.
"Gaskiya a ce akwai jagora guda ɗaya zai yi wuya kasancewar kowane ɓangare yana jan ragamar jama'arsa amma idan buƙata ta haɗo su za ka gan su tare kamar babu wata matsala su kuma tunkari ita buƙatar musamman idan wata barazana misali kamar lokacin da suka ga yiwuwar shigar Rabi'u Kwankwaso APC. Wannan ya sa suka ajiye dukkan banbancin da ake gani akwai tsakaninsu."
Daga ƙarshe malam Kabiru Sufi ya ƙara da cewa "gane ɓangaren da ya fi yawan mabiya shi ne wani abun da ba za a iya tabbatarwa a yanzu haka ba."











