Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa shigar malamai siyasa ke janyo muhawara a arewacin Najeriya?
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana muhawara a Najeriya musamman a shafukan sada zumunta bayan da fitaccen malamin Addinin Musulunci, kuma tsohon ministan sadarwa Sheikh Ali Pantami ya sake motsa siyasarsa.
A ƙarshen makon da ya gabata ne malamin ya je harabar sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Gombe inda ya sabunta rajistarsa.
Tsohon ministan sadarwar ya kuma zagaya sassan birnin Gombe bisa rakiyar dubban magoya bayansa.
Wannan ba shi ne karon farko da shigar malaman Addinin Musulunci harkar siyasa ya janyo muhawara a tsakanin al'umma ba.
Rawar da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ke takawa a fagen siyasar jihar abu ne da ya daɗe yana haifar da muhawara.
Haka nan ma a lokuta da dama akan tsangwami malaman addinin Musulunci da ke tattaunawa kan lamuran siyasa a lokutan wa'azi ku huɗubobi, inda ake ganin tamkar 'suna shiga wani fage da ba nasu ba'.
Duk da kasancewarsa Ali Pantami tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, da dama ƴan ƙasar ba sa yi masa kallon ɗansiyasa, a maimakon haka suna ganin Buhari ya naɗa shi muƙamin ne domin ƙwarewarsa a fannin sadarwa.
'Na jima da shiga siyasa'
Sai dai kalaman da Sheikh Pantami ya yi lokacin sabunta rajistar tasa sun kawar da wannan tunani.
''Wasu na yi min kallon ba mu jima da shiga siyasa ba, amma maganar gaskiya ana damawa da mu a harkokin siyasa tun 2001''.
''Ka san ita siyasa kamar jami'an tsaro ne, akwai masu yunifom akwai kuma marasa yunifom, to mu ƴansiyasa ne marasa uninfom'', kamar yadda ya bayyana a gaban ɗimbin magoya bayansa.
Ana dai alaƙanta malamin addinin - wadda ƙwararren masanin sadarwa ne - da tsayawa takarar gwamman jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Tun bayan faruwar wannan al'amari ƴan ƙasar da dama suka riƙa bayyana ra'ayoyinsu game da shigar malamin siyasa, inda wasu ke goyon bayan wasu kuma ke adawa da matakin.
Me ya sa wasu ke ganin rashin dacewar shigar malamai siyasa?
Farfesa Kamilu Sani Fagge mai sharhi kan al'amuran siyasa kuma malami a Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce fargabar zubewar kimar malaman ce ta sa wasu ke ganin rashin dacewar shigarsu siyasa.
''In da za su shiga kuma su riƙe martabar da suke da ita, kuma su yi amfani da iliminsu na addini, to da ba wanda zai ce bai dace ba, amma su shiga su goyi bayan azzalumai ko rashin adalci, to wannan shi ne abin da mutane ke fargaba'', in ji malamin jami'ar.
Shi kuwa Dokta Aliyu U. Tilde mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce abin da ya sa wasu ke ganin rashin dacewar shigar malaman addini siyasa a arewacin Najeriya asali ya samo.
Ya ce tun asali tsarin mulkin arewacin ƙasar ya nuna cewa sarakuna da limamai da malamai kowa na taka rawa daban-daban ne.
''A karon farko rawar da malamai ke takawa ta karantarwa ce, inda suke karantar da littafafi, haka aka tafi har lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka''in ji shi.
Dokta Tilde ya ce bayan zuwan Turawa sai ya zama duk wanda suke cikin siyasar ƴan boko ne.
''A wannan lokacin duk waɗanda suke cikin siyasar ba malamai ba ne ƴan boko ne irin su Ahmadu Bello Sardauna, da Tafawa Ɓalewa da su Mallam Aminu Kano da Sa'adu Zungur, duka ƴan boko ne'', in ji shi.
Tsohon kwamishin Ilimin na jihar Bauchi ya ce a haka aka taho har yau, malamai na gefe suna karantarwa, ƴanboko na cikin siyasa tsundum.
''To wannan shi ya ɗore har aka zo lokacin su Shagari a Jamhuriya ta biyu haka ma a farkon jamhuriya ta huɗu, duka malamai sun ja gefe ba ruwansu da siyasa'', in ji shi.
Ya ce wannan ne dalilin da ya sa har yanzu wasu ke ganin bai kamata malamai su shiga harkokin siyasa ba.
''Musamman saboda an san akwai mugayen ɗabi'un da ke tattare da harkokin siyasar Najeriya'', in ji shi.
Dokta Tilde ya ƙara da cewa zaluncin da ake yi a tsarin siyasar ne ya sa wasu ke ganin rashin dacewar shigar malaman addini harkokin siyasar.
Ya dace malamai su shiga siyasa?
Masu sukar shigar malamai siyasa na kafa hujja da yanayin yadda tsarin siyasar Najeriya ya gurɓace da munanan ɗabi'u, kamar cin hanci da rashawa da cin amana da amfani da ƴan dabar siyasa.
In da suke ganin zai yi wahala malaman su iya kauce wa faɗa wa miyagun ɗabi'un.
To Amma Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ya ce dalilin da ya ce wasu ke ganin baiken malaman da suka shiga siyasa shi ne ana fargabar za su sauka daga koyarwar addinin da suke kira a kai.
''Ana ganin kamar za su sauka daga koyarwar addinin, su kuma bi yarima domin shan kiɗa, inda a ce za su tsaya a kan martabar da suke da ita su kuma yi amfani da iliminsu na addini wajen saita alƙiblar siyasarsu, to da ba wanda zai ce kada su yi'', in ji malamin Jami'ar.
A nasa ɓangare Dokta Tilde ya ce a ganinsa indai mutum ya haɗa ilimin addini da na zamani to shi ne ma ya fi cancanta ya shiga siyasar ƙasar.
''Yana da kyau a ce mutum yana da ilimin addini sannan ya siffantu da tsaron Allah, da riƙon amana, sannan ya kasance yana da ilimin zamani'', in ji shi.
Ya ce inda mutum ya mallaki waɗannan abubuwa to babu wanda ya canci a ba shi amanar al'umma fiye da shi.
Dokta Tilde ya ƙara da cewa a halin da ake ciki yanzu na ƙoƙarin yin gyara a harkar zaɓen ƙasar yana da kyau malamai su shiga siyasa.
''To da malamai masu ƙwarewar su shiga siyasar su yi mulki, da kuma a bar ƙasar hannun marasa ilimin addinin wanne ya fi?''.
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ɗin ya kuma ɗora alhakin halin da ƙasar ke ciki - na taɓarɓarewar tsaro da matsin tattalin arziki - kan shugabannin da ya bayyana da ''marasa tsoron Allah''.
Haka ma Farfesa Kamilu Fagge ya ce idan har za a bar fagen siyasa ga mutane marasa ɗabi'u masu kyau, to za a samu matsala.
''In dai addinin mutum zai yi tasiri, to wannan abu ne da ake maraba da shi'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce a rewacin ƙasar ne, inda adinin musulucni ke da rinjaye, ake sukar malaman addinin da suka shiga siyasa.
''Yanzu idan ka duba kudancin ƙasar nan akwai manyan malaman Addinin Kirista da suka shiga siyasa har ma aka zaɓe su manyan muƙamai'', in ji shi.