Sifaniya ta kai zagayen semi fayinal bayan doke Jamus a gasar Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Sifaniya ta yi nasarar tsallakawa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 bayan doke masu masaukin baƙi Jamus 2-1.
Wannan na ɗaya daga cikin wasannin da ake hanƙoron gani a gasar ganin yadda tawagogin biyu suka zama mafiya hazaƙa, kuma wasan bai ba wa 'yan kallo kunya ba.
Dani Olmo ne ya fara ci wa Sifaniya ƙwallo a minti na 51, inda har sai da ta kai saura minti biyu lokaci ya cika sannan F. Wirtz ya farke wa Jamus.
Kazalika, 'yan ɗaƙiƙoƙi ne suka rage a shiga bugun finareti bayan cikar zagayen ƙarin lokaci Mikel Merino ya lallaɓo ya cinye Jamus da ka bayan Olmo ya bugo ƙwallo a sama.
Yanzu Sifaniya za ta jira wanda ya yi nasara a wasan da Faransa take ɓarje gumi da Portugal yanzu haka a ɗaya wasan na zagayen kwata fayinal.







