Dan Najeriyar da zai raka biloniyan Japan yawon shakatawa duniyar wata

Asalin hoton, DEARMOON.EARTH
Wani dan Najeriya da kasar Czech Yemi Akinyemi Dele wanda aka fi sani da Yemi AD ya samu damar shiga cikin jerin tawagar da za su je duniyar wata a 2023 tare da biloniyan nan dan kasar Japan Yusaku Maezawa.
A 2018 ne, attajirin ya saye duka kujerun kumbo da kamfanin Elon Musk ya hada wadanda za su tafi duniyar wata na tsawon mako guda kafin su dawo.
Mai arzikin yace yana son mutane masu basira su kasance tare da shiyayin tafiyar, a watan Maris din 2021 ne ya sanar da cewa yana son mutane takwas da za su kasnce cikin tawagar daga fadin duniya.
Da yake sanar da sunayen matafiyan, shugaban tawgaar Maezawa wanda aka fi sani da MZ yace: "Ina matukar farin cikin sanarsunayen wadan nan mutanen da za su shiga cikin ayarin tafiyata zuwa duniyar wata."
Sun zabi mutanen ne daga cikin miliyoyin da suka nemi wannan dam a fadin duniya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Wane ne Yemi Akinyemi Dele?
A bayanin da yake kan shafinsa na tafiya duniyar watan ya ce, "Ina yin wannan ne domin tunatar da yaranmu masu basira cewa duk tafiyar da kafara, ka zama kana da manufa a cikinta, dole ka nuna cewa burikanka za su iya zama gaske, ka tabbatar da burinka ba shi da iyaka."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mahaifin Yemi Akinyemi Dele dan Najeriya ne mahaifiyarsa kuma yar Jamhuriyar Czech ce. An haife shi a Czech a bayaninsa kuma yace yana wakiltar gabashin Turai ne da Afrika.
An haifi Yemi ne a 1981 kuma yana da kwarewa a bangarorin rayuwa da yawa, yana kirkire-kirkire yana kuma koyar da rawa ga yara, yana koyawa mutane da kungiyoyi yadda ake kirkire-kirkire.
Yemi AD yace lokacin da MZ ya sanar a cikin wani taro na zoom cewa ya zabe shi cikin wadanda za a tafi da su, nan take ya sanya ihu ya tshi ya fara rawa ya ma manta da cewa Attajirin na cikin taron, mutanen da ke tare da MZ suka barke da dariya. Yace nan ya zauna yake jin abin kamar wani mafarki.
Yemi AD yace mutum na karshe da yaje duniyar wata ya je ne tun gabanin a haife shi.
"Babbar girmamawa ce, babbar dama ce, ba gare ni ba kawai ga duk wani dan kasar Czech haka ga mutanen Najeriya, da kuma yaranmu masu tasowa," in ji Yemi AD.
Yemi AD wanda ya fito daga iyalai masu matsagaicin karfi, wannan damar da ya samu zuwa duniyar wata wani gwarin gwiwa ne ga matasan da ke tasowa, yace hakan zai taimaka musu wajen cikar burikansu, su kuma kai ga inda suke son kai wa.
Yemi AD ya ce kullum firgici kara kama shi yake indai ya tsaya gaban kumbon da zai dauke su.
Amma yace da yara matasa za su samu irin wannan damar da ya samu za su fi shi kwarin gwiwa domin ba su da tsoro kamar manya.
Yace wannan tafiyar ta shi ba kawai ga mutanen da suke koyar rawa ba ne ya wuce gaban haka.










