Ma'anar cinikin sassan jikin ɗan Adam, tasirinsa da haɗarinsa

Kidney graphic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoto yadda ƙodar dan Adam take

Ma'anar cire sassan jikin ɗan Adam ya ja hankulan ƴan Najeriya masu yawa.

Hukumomin Birtaniya sun kama wasu fitattun ƴan Najeriya biyu bisa tuhumar suna kokarin cire sassan jikin wani mazaunin ƙasar.

Shin me ake nufi da sassan jikin ɗan Adam?

Wannan labarin zai sanar da mai karatu cikakken ma'anar sassan jikin ɗan Adam.

Ma'anar cire sassan jikin ɗan Adam

Cire sassan jikin ɗan Adam tamkar kisan mutumin da ke da jikin ne, domin cinikayya ce ta sassan jikin ɗan Adam domin a dasa su a jikin wasu masu bukata.

Wannan fassara ita ce ƙungiyar ƙasa-da-ƙasa mai kare hakkin ɗan Adam ta fitar.

Sun ce akan yi wannan mummunar ɗabi'a ta cire sassan dan Adam a kasashe masu yawa na duniya, musamman a China da Indiya da kuma yankin Sinai.

Cire sassan ɗan Adam na nufin yin tiyata domin a cire sassan ɗan Adam ba tare da amincewarsa ko na hukuma ba, daga nan sai a dasa wa wani ko wasu mutanen.

Sai dai ya kan faru da amincewar wanda aka cire wa sashin jikin a wasu lokutan.

Yana kuma nufin cire sassan jikin wani wanda bai dade da mutuwa ba, kuma a adana su domin dasawa wasu masu rai da ke bukatar sassan jikin.

Wadanda ake cire wa sassan jiki

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai mutanen da ke amincewa su sayar da sassan jikinsu ga masu safarar sassan jikin ɗan Adam a kasuwar bayan fage domin a biya su wasu kuɗaɗe, kamar yadda wata mujalla mai suna Delta-net.

Ciniki ne mai gwaɓi sosai domin a misali akan sayi koɗar ɗan Adam a kan dalar Amurka 150,000.

Masana kiwon lafiya na cewa kowane ɗan Adam mai lafiyayyun ƙoda biyu na iya rayuwa da ƙoda guda ɗaya bayan an cire ɗayar, sai dai ba haka lamarin yake a ko yaushe ba.

Akwai wadansu mutanen da ake cire wa sassan jinsu da karfin tsiya.

A misali: Akan sace wasu mutanen kuma su gane cewa an cire wani sashen jikinsu ba tare da saninsu ba.

A kan kuma yaudari wasu mutanen, a ce musu suna bukatar tiyata domin warkewa daga wata cuta, amma yayin da ake musu tiyatar sai a cire wani sashen jikin nasau ba tare da saninsu ko amincewarsu ba.

Kuma saboda tururuwar da 'yan gudun hijira ke yi zuwa nahiyar Turai, akan yi wa masu kokarin shiga kasashen alkawarin izinin shiga nahiyar idan suka yarda a cire wani sashe na jikinu.

Kuma akwai wadanda aka cire wa sassan jiki da a baya an shigar da su Turai ne ta barauniyar hanya.

Akwai wadanda ake yin odar a kashe su, sannan a cire sassan jikinsu domin biyan bukatar wasu miyagun mutane.

human anatomy graphic

Asalin hoton, Getty Images

Haɗarin cire sassan jikin ɗan Adam

Cire sassan jikin ɗan Adam abu ne mai matukar hdari saboda babban aikin tiyata a ke yi wa wanda aka cire sashen jikin na shi.

A misali, wanda aka cire wa ƙoda na iya fuskantar:

  • Tsananin zafin jiki
  • Daskarewar jini
  • Bayyanar kwayoyin cuta
  • Cutar sanyin kashi
  • Lalacewar huhu
  • Kamuwa da matsalar dimuwa
  • Jikinsa na iya biirewa magani
  • Mutuwa

Wuraren da aka fi cire wa mutane sassan jikinsu

Akwai kasashen da aka fi yin wannan mummunar sana'ar cikin kasashen duniya.

Kasashen sun hada da China da Indiya da yankin Tuddan Sinai.

Ana kuma yin haka ma a kasar China.

Akwai hujjar da ke cewa wasu hukumomin gwamnatin kasar na kawar da kai yayin da ake kashe mutane domin amfana da sassan jikinsu.

A shekarar 2017, hukumar da ke yaki da masu safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP ta ce za ta fara sa ido sosai kan yadda ake safarar mutane domin sace musu sassan jikinsu a ciki da wajen kasar.

A karshen 2021, wani rahoto ya ce an gano wani wuri a Libya inda ake tsare da bakaken fata 'yan Afirka kuma 'yan ci-rani a cikin keji tamkar dabbobi.

Shugaban hukumar ta NAPTIP ya kuma ce ana sace sassan jikin mutanen kamar idanu idanunsu da kodarsu da kuma huhunsu, sannan a sayar da su a akasuwar bayan fage zuwa kasashen nahiyar Turai.

Shin cire sassan jiki ba laifi ne ba kuwa?

A halin yanzu kasa daya ce kawai ta amince a rika cinikin ƙoda: Ita ce ƙasar Iran.

Amma a wasu kasashen, mutum na iya ba wani ko wata wani sassan jikinsa (ciki har da ƙodarsa) idan ya so, amma ba domin za a biya shi da kudi ba.

Wasu mutane kan ba 'yan uwansu wasu sassan jikinsu domin taimaka musu yayin da suke fama da wata matsalar rashin lafiya.

Sanan ba laifi ba ne mutum ya ba wani mutum na daban, wanda bai ma san shi ba wani sashe na jikinsa a matsayin taimakon jin kai.

A wani yanayin, ba a biyan kowa kudi ko lada, saboda haka ba daidai ba ne a yi kuskuren hada wannan da wanda ake cire sassan jikin dan Adam ba tare da amincewar mai su ba.