Yadda ta kasance tsakanin Shugaba Buhari da firaminstan Birtaniya a taron CHOGM

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jaddada wa Firaminista Boris Johnson na Birtaniya aniyarsa ta sauka daga mulki a shekarar 2023 bayan manyan zaɓukan ƙasar.
Buhari ya gaya wa firaministan hakan ne a yayin wata ganawar diflomasiyya da suka yi a wajen taron ƙasashen renon Ingila CHOGM, a ƙasar Rwanda.
A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ranar Alhamis, ta ce Boris Johnson ne ya tambayi Buhari ko zai sake tsayawa takara, “wataƙila don bai san yadda tsarin Najeriyar yake ba”.
Amma sai Shugaba Buhari ya amsa da cewa “Ni na yi tazarce? A’a! Ko wanda ya yi ƙoƙarin zarcewa ma ai bai ƙare ƙalau ba.”
Batun Kanu

Asalin hoton, Getty Images
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
A kan batun jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB kuwa, wanda firaminsitan ya tambayi Buhari kan hana Nnamdi Kanun gana wa da lauyoyinsa, shugaban ƙasar ya yi watsi da zargin.
Ya ce an bai wa Kanu duk wata dama da doka ta tanada don ya yi bayani kan abubuwa “marasa dadi” da ya dinga faɗa a kan Najeriya lokacin da yake Birtaniya.
“Yana ganin ya tsira a Birtaniya har ya dinga faɗar abubuwa marasa daɗi a kan Najeriya.
"Daga ƙarshe muka kamo shi bayan barinsa Birtaniyan muka aika shi kotu. Don ya je ya kare kansa.
"Lauyoyinsa na da damar ganinsa. Ka tuna cewa ya taɓa tserewa, ta yaya za mu tabbatar ba zai sake aikata hakan ba idan aka sake ba shi beli?, in ji Buhari.
"Kun kasa maganin matsalar tsaron Libya"

Asalin hoton, Buhari Sallau
Sanarwar fadar shugaban Najeriyar ta kuma ce Firaminista Johnson ya nuna zaƙuwar ƙasarsa ta taimaka wa Najeriya a fannin tsaro.
Amma sai Shugaba Buhari ya ce: “Da tun farko an taimaki Libiya da abubuwa ba su lalace ba.
“Rushewar gwamnatin Muammar Gadaffi bayan shekara 42 a mulki ya sa dakarunsa sun watsu a yankin Sahel, kuma suna yin ɓarna a ko ina, don ba abin da suka sani sai harba bindigogi,” a cewarsa.
Boko Haram
Batu na gaba da Boris Johnson ya yi wa Buhari shi ne na rikicin Boko Haram, inda shugaban Najeriyar ya ce gwamnati na matuƙar ƙoƙari wajen ilimintar da mutane cewa marar hankali ne kawai zai kashe mutane “yayin da yake kiran sunan Allah.
“Allah adali ne. Ba za ka kashe rayuka sannan ka alaƙanta hakan da Allah ba.
"Kuma an ci gaba da ilimintar da mutane don su gane cewa Boko Haram ba hanyar Allah ba ce, ba kuma addini ba ne.
Jin dadin kasuwanci

Asalin hoton, Buhari Sallau
Haka kuma fadar Najeriya ta ce Firaminista Boris Johnson ya bayyana jin daɗinsa kan dangantakar kasuwanci da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ya kuma sha alwashin cewa Birtaniya na ƙoƙarin rage haraji a kan wasu kayayyakin da ake shigar wa Najeriya.
Mista Johnson ya bayyana alaƙar ƙasashen biyu a matsayin mai ƙarfi, yana mai cewa “Ina so na tabbatar da cewa muna yi abin da ya dace sosai.
"Babbar haɗin gwiwa ce a gare mu, kuma ya kamata mu amfana da ita.
A ƙarshe firaministan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa kan wasu hare-hare na baya-bayan nan da aka kai Najeriya, “musamman na coci-coci,” kamar yadda sanarwar ta faɗa.










