Me ya sa har yanzu Najeriya ta kasa rabuwa da talauci?

Wani mutum na ƙirga kudi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Masana tattalin arziki da masu sharhi na ci gaba da muhawara kan rahoton da Bankin Duniya ya fitar game da yadda talauci ke ci gaba da samun wurin zama a ƙasar.

Rahoton na Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya na cikin ƙangin talauci duk da cewa an samu bunƙasa a tattalin arziƙin ƙasar da ƙaruwa a samun kuɗaɗen shigar ƙasar.

Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da rahoton a Abuja, babban daraktan ƙasa na Bankin Duniyar, Mathew Verghis ya ce gyare-gyaren Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba.

Babbar cibiyar kuɗin ta duniya ta ce sama da mutum miliyan 139 a Najeriya na rayuwa cikin talauci a shekarar 2025, duk da matakan gyaran tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka.

Sai dai Bankin ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin Najeriya zai bunƙasa da kashi 4.4 cikin 100 a shekarar 2027.

Wannan na zuwa ne bayan makonni kaɗan da Tinubu ya yaba wa gwamnatinsa bisa abin da ya kira "sake farfaɗowar tattalin arziƙin ƙasa.

Cikin wani jawabi da Tinubu ya yi a ranar bikin yancin kai ya ce gyare-gyaren tattalin arziƙi da zamantakewa da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da kyakkyawan sakamako.

Martanin gwamnatin Najeriya

Bola Tinubu zaune a ofishinsa ya yi tagumi, sanye da gilashi

Asalin hoton, Bola Tinubu Facebook

Gwamnatin Najeriya ta nuna rashin gamsuwarta kan rahoton na Bankin Duniya inda ta yi watsi da shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce ƙididdigar ba ta nuna haƙiƙanin halin da ake ciki a ƙasar ba.

''Bankin Duniya ya yi amfani da ƙa'idar duniya wadda ke ɗaukar duk wanda ba ya samun sama da dala 2.15 a rana a matsayin talaka'', a cewar fadar gwamnatin Najeriyar.

Ta ci gaba da cewa ''wannan ƙa'ida an kafa ta ne tun shekarar 2017, kuma idan aka fassara ta zuwa kuɗin Najeriya a yau, ta kai kusan Naira 100,000 a wata fiye da sabon mafi ƙanƙanta albashi na Naira 70,000 kenan''.

''Bayanan da Bankin Duniya ya dogara da su tsofaffi ne tun daga shekarar 2018/2019, kuma ba su haɗa da tattalin arzikin yanzu ba. Saboda haka, gwamnati ta bayyana cewa wannan adadi misali ne na ƙididdigar duniya, ba ainihin yanayin da ake ciki a shekarar 2025 ba."

Daga ƙarshe fadar shugaban Najeriyar ta ce gwamnatin Shugaba Tinubu na mai da hankali ne wajen rage wahalar tattalin arziki ta hanyar shirye-shirye na musamman kamar tallafin kuɗi ga talakawa, da bashin karatu na ɗalibai, da sauransu.

Me Bankin Duniyar ya dogara da shi?

Wani mutum na ƙirga bandiran kuɗin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Masu sharhi da masana tattalin arziki na ci gaba da bayyana ra'ayinsu dangane da abubuwan da Bankin Duniya ya dogara da su wajen fitar da bayanan da ke cikin rahoton nasa.

Dr. Abdurrazak Ibrahim Fagge, Malami ne a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar North West da ke Kano ya kuma ce Bankin duniyar ya dogara ne da wasu abubuwan da ba na Najeriya ba.

Abubuwan da Bankin ya dogara da su sun haɗa da:

  • Yaƙin Ukraine

Yaƙin Ukraine ya shafi farashin abinci a faɗin duniya, sakamkon yadda ƙasashen biyu ke kan gaba wajen samar da abinci a duniya.

''Wannan yaƙi ya haifar da tsaiko da dama wajen jigilar kayan abinci daga ƙasashen biyu zuwa nahiyar Afirka'', in ji masanin tattalin arzikin.

  • Annobar Covid

Annobar Covid-19, wata babbar matsala ce da ta shafi tattalin arzikin duniya.

A lokacin annobar an kulle ko'ina da zirga-zirga tsakanin ƙasashe, wani abu da ya haifar da tsaiko ga tattalin arzikin duniya.

  • Harajin Trump

Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge ya ce haraje-harajen da shugaban Amurka, Donald Trump sanya wa wasu ƙasashen duniya sun taimaka wajen ƙaruwar farashin wasu kayayyaki a duniya.

Masanin tattalin arzikin ya ce wannan al'amari ya haifar da ƙaruwar talauci tsakanin ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki ciki har da Najeriya.

  • Yaƙin Gabas ta Tsakiya

Daya daga ciin abubuwan da Ankin duniya ke auna tattalin arziki shi ne farashin man fetur a kasuwannin duniya, kamar yadda Dr Fagge ya yi ƙarin haske.

''Idan ka dubi wannan yaƙi akwai lokutan da ke yake shafar fitar da mai musamman daga ƙasashen yankin masu arzikin man, wanda kuma hakan na shafar farashinsa a duniya'', in ji shi.

Da gaske talauci ya ƙaru a Najeriya?

robobi cike da kayan miya da albasa da dankalin turawa da doka da kuma kiren na kwai

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Abdurrazak Ibrahim Fagge ya ce a ɓangarensu na masana tattalin arziki suna ganin kamar hasashen na Bankin Duniya na kan hanya, domin kuwa bai zo musu da mamaki ba.

''Wannan rahoto ba abin mamaki ba ne, musamman idan a Najeriya kake rayuwa kuma kana zuwa kasuwanni, sannan kana shiga yankunan da talakawan ƙasar ke rayuwa'', in ji shi.

Masanin tattalin arzikin ya kuma alaƙanta matsalar da wasu matakai da ya ce gwamnatin Najeriya ta ɗauka bisa shawarar Bankin Duniya, kamar cire tallafin man fetur da barin naira ta nemo wa kanta daraja.

''Shi Bankin Duniya na ganin waɗannan matakai za su taimaka wajen raguwar talauci a Najeriya, amma saɓanin haka, mu abin da muke gani, su ne ma suka ƙara jefa ƙasar cikin talauci'', in ji shi.

Ya ce batun cire tallafin man fetur ya sa talakawan ƙasar da dama sun ji a jikinsu, sakamakon yadda farashin abubuwa da dama suka sauya a lokaci guda.

''Haka ma idan ka duba batun barin kasuwa ta yi halinta kan farashin dala, a lokacin farashin dala na naira 770, kuma a hakan ma talakawan ƙasar na kuka, amma da aka fara amfani da tsarin, sai ta ƙara tashi zuwa fiye da 1,500, kodayake a ƴan kwanakin nan ta sauko'', in ji shi.

Dr Fagge ya ce bisa bayanan na Bankin Duniya za iya cewa talauci ya ƙaru a Najeriya, kuma al'ummar ƙasar sun ƙara shiga halin matsi da talauci.

Masanin tattalin arzikin ya kuma ce Bankin Duniyar ya gina rahoton nasa ne a kan rahoton da hukumar kididdiga ta kasar NBS ke fitarwa lokaci zuwa lokaci.

Dakta Fagge ya ce wani abu da ya ƙara fitowa fili a cikin rahoton shi ne raguwar giɓi tsakanin masu kuɗi da talakawa.

Sai dai ya ce raguwar da aka samu abin nan ne da Hausawa ke cewa ci gaban mai haƙar rijiya.

''Ba wai talakawan ba ne suka samu kuɗi, a a su talaucinsu ƙaruwa ma ya yi, sannan su kuma masu kuɗin wasu daga cikinsu sun koma cikin rukunin talakawa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Me gwamnati za ta yi don magance matsalar?

Wani mutum na ƙirga kuɗi

Asalin hoton, Getty Images

Dr Fagge ya ce abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi shi ne ɗaukar matakan da suka dace domin rage talauci da rashin aikin yi a ƙasar.

  • Daidaita farashi

Masanin tattalin arzikin ya ce yana da kyau gwamnati ta ɗauki matakin kawo daidaito a farashin kayyaki a ƙasar.

Hakan zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kaya da ake yawaitar samu a lokaci zuwa lokaci, kamar yadda ya bayyana.

  • Samar da ayyukan yi a ƙasar

Abu na biyu da malamin jami'ar ya bayyana a matsayin mafita daga talauci a Najeriya shi ne samar da ƙarin ayyukan yi ga 'yan ƙasar.

Masanin ya ce akwai saɓani a alƙaluman rashin aikin yi a Najeriya tsakanin Bankin Duniya da hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS.

''Akwai rahoron Bankin Duniya da ya nuna cewa kimanin mutum miliyan 100 ne ke fama da talauci a Najeriya, amma kuma idan ka duba rahoton NBS yana cewa rashin aikin yi bai wuce kashi biyar cikin 100 ba''.

Dr Fagge ya zargi gwamnatin Najeriyar da sanya baki a rahoton alƙaluman da NBS ke fitarwa.

''An sauya tsare-tsare na yadda ake tattara alƙaluman, misali a baya duk wanda ya yi aiki na ƙasa da sa'a a 20 a mako biyu ana lissafa shi a cikin marasa aikin yi, amma a yanzu duk wanda ya yi aikin sa'a ɗaya cikin mako biyu ana lissafa shi cikin masu aikin yi'', in ji Dr Fagge.

Ya ce wannan dalilin ne ya sa alƙaluman ayyukan yi suka zaftaro daga kimanin kaso 40 zuwa kaso 4.1.

Masanin ya ce haka ma ake lissafa alkaluman arzikin ƙasar.