Za a hukunta duk wanda ya azabtar da 'yan Syria - Jagoran 'yantawaye

 Abu Mohammed Al- Jolani

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 3

Babban jagoran kungiyar 'yantawayen Syria Abu Mohammed Al- Jolani, ya sanar da cewa za a tuhumi manyan jami'an hambararriyar gwamnatin Bashar al- Assad da ke da hannu wajen azabtar da fursunonin siyasa.

Jagoran 'yantawayen ya bayyana haka ne a wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara.

Abu Mohammed Al-Jolani, wanda a wannan karon ya yi amfani da sunansa na ainahi, Ahmed al-Sharaa a sakon da ya sanya na wannan sanarwa ta shafin Telegram, ya ce duk wani babban jami'i a tsohuwar gwamnatin ta Bashar al-Assad da yake da hannu a azabtar da 'yansiyasar da aka tsare zai yaba wa aya zaki.

Ya ce za a bincike shi tare da hukunta shi daidai da abin da ya aikata.

Al-Jolani ya kara da cewa ko da jami'in ya tsere daga kasar ta Syria za su nemi kasar da ya je ta taso keyarsa ya dawo.

Sai dai sanarwar ta jaddada cewa, duk wanda ba shi da hannu a wannan ta'asa ba zai fuskanci hukunci ba.

A ranar Litinin ne Al- Jolani, ya gana da tsohon Firaministan Syriar domin tsara yadda gwamnati za ta sauya hannu.

A halin da ake ciki kuma dubban jama'ane a kasar ta Syria suka yi tururuwa zuwa kofar wani gidan yari da ake tsare fursunonin siyasa, domin neman 'yan uwansu.

'Yantawayen sun ce tuni daman sun saki sama da mutum dari daya daga gidan kason na Saydnaya, da ke wajen babban birnin kasar Damascus, to amma da dama babu labarinsu.

Jami'an rundunar tsaro da agaji ta kasar, sun ce sun bincike dakunan kurkukun, har da na karkashin kasa a gidan sarkar amma kuma ba su ga kowa ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abubuwan da ke ta wakana a kasar ta Syria na zaman wani gagarumin sauyi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda da dama a yankin ke sa ido su ga me zai wakana yayin da ake kara nuna damuwa kan zaman lafiya.

Lebanon ta ce za ta rufe dukkanin iyakokinta da Syria in banda daya kawai da za ta bari.

Haka ita ma Jordan ta rufe kan iyakarta da Syria, Isra'ila na gargadin mazauna kauyukan kudancin Syria yayin da sojojinta suka kwace iko da wani yankin tudun-mun-tsira da ke Tuddan Golan.

Kafofin yada labarai na kasar ta Syria sun ce Isra'ilar ta kai gomman hare-hare a fadin kasar ciki har da babban birnin Damascus.

Kuma wata cibiyar bincike da ake zargin ana hada makamai masu guba na daga cikin inda ta kai harin.

Isra'ilar ta ce ta yi hakan ne domin ganin makamai ba su fada hannun masu tsattsauran ra'ayi ba.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce hakan ya zama dole domin Isra'ilar na neman kare kanta.

Ya ce, ''suna daukar duk matakan da suka wajaba ne domin tabbatar da tsaronsu, dangane da sabon yanayin da aka samu a Syria.''