Yadda kasuwancin gaɓoɓin gawawwakin mutane ke kawo riba mai tsoka a Amurka

- Marubuci, Luke Mintz
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Harold Dillard yana ɗan shekara 56 a lokacin da aka gano yan da cutar kansa mai haɗari a mararsa a watan Nuwanban 2009. Cikin 'yan makonni kuma sai ga shi ya shiga halin rai-kwaikwai-mutu-kwakwai.
Kwanaki kaɗan kafin ya mutu, wani kamfani mai suna Bio Care ya kai wa Mista Dillard ziyara a wurin kula da lafiyarsa. Sun tambaye shi ko zai iya sadaukar da gawarsa domin aikin tiyatar sauya gwiwar mutum.
Kamfanin ya ce zai ƙona ɓangaren jikinsa da ba a yi amfani da shi ba kuma ya mayar wa iyalainsa kyauta.
"Idanunsa sun firfito," a cewar 'yarsa Fara fasold. "Yana ganin yin hakan kamar wani sauƙi ne ya sama wa danginsa. Sadaukar da gawarsa abu ne mai kyau da zai yi na ƙarshe kafin ya mutu."
Hakan kuwa aka yi, kuma 'yan watannin mutuwar tasa sai 'yansanda suka kira 'yarsa suna faɗa mata cewa sun ga ƙoƙon kan mahaifinta.

A wurin ajiyar kayayyaki na kamfanin, 'yansanda sun ce sun gano sassan jiki sama da 100 na muutm 45.
Farrah ta ce ta zaci za a mutunta gawar mahaifinta amma sai aka "gididdiba" ta kawai.
Kamfanin ya faɗa ta bakin lauyansa cewa ba su gididdiba gawar mutane. Yanzu kamfanin ba ya aiki, kuma ba a iya samun tsofaffin ma'aikatansa domin su yi ƙarin bayani.
Wannan karon farko da Farrah ta fara jin dillalan gawa: wato kamfanoni masu zaman kansu da ke karɓar gawa, su daddatsa ta, kuma su sayar da gaɓoɓin domin samun riba daga masu bincike irin na kimiyya.
Hada-hadar gawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun daga ƙarni na 19 lokacin da aka faɗaɗa koyon aikin likitanci, wasu suka fara jin cewa za su iya sadaukar da gawarsu domin yin bincike na kimiyya da ita.
Brandi Schmitt shugabar wani shiri ce na bayar da sadakar gaɓoɓi a Jami'ar California. Ta ce a shekarar da ta gabata ta samu sadakar "cikakkun gawa 1,600", kuma suna da jerin sunayen mutum 50,000 da suka amince su yi hakan.
Ta ce abu ɗaya ne ke jawo mutane su ba da gudummawar gawa: "Akasarin mutane na da ilimi ko kuma suna sha'awar harkokin koyar da ilimin."
Amma kuma akwai maganar kuɗi ma. Jana'iza na da tsada sosai, Ms Schmitt ta ce: "Akasarin mutane na ganin ɗaukar gawarsu ba tare da kashe ko ƙwandala ba zai fi sauƙi."
Kamar sauran makarantun kiwon lafiya, Jami'ar california ba ta samun riba daga gudummawar gawarwakin da take karɓa.
Sai dai a kwanan nan wasu dillalan gawa sun fara yawa a Amurka, inda suke karɓar gawarwakin mutane, su daddatsa su kuma su sayar.
Daga cikin kwastomominsu akwai jami'o'i da ke amfani da su wajen horar da likitoci. Sauran kuma sun ƙunshi injiniyoyi da ke gwada sabbin kayayyaki da suke ƙirƙira.
Sai dai Birtaniya da ƙasashen Tarayyar Turai sun haramta cinikin gawa don riba, yayin da rashin dokoki masu tsaruri a Amurka suka ta'azzara lamarin.
Wani bincike da ɗanjaridar Reuters Brian Grow ya gudanar a 2017 ya gano kamfanonin dillancin gawa 25 a Amurka. Ɗaya daga cikinsu ya samu dala miliyan 12.5 cikin shekara uku.
Hada-hadar ƙasashen duniya
Kasuwancin ya haɓaka ne saboda ƙarancin dokoki a Amurka, in ji Jenny Kleeman, wadda ta shafe shekaru tana bincike kan lamarin domin rubuta littafinta mai suna The Price of Life.
Yayin da dokar Human Tissue Act a Birtaniya ta haramta duk wata hanya da mutum zai samu kuɗi da dillancin gawa, babu irin wannan dokar a Amurka. Duk da cewa dokar Uniform Anatomical Gift Act a Amurka ta hana sayar da gaɓar jikin mutum, dokar ce dai kuma ta bai wa mutum damar cajar "kuɗi maras yawa" domin "sarrafa" gaɓar mutum.
Waɗannan dokokin ne suka mayar da Amurka cibiyar dillancin gawa. A littafinta, Kleeman ta gano cewa wani kamfanin Amurka kan yi safarar sassan mutum zuwa ƙasashen dunya 50, ciki har da Birtaniya.
"A ƙasashe da dama, akwai ƙarancin gudumawar gawa," a cewar Kleeman. "Kuma daga Amurka suke samun gawar."
Babu rajistar masu dillancin gawa a hukumance kuma da wuya a iya samun alƙaluma a kansu. Amma kamfanin labarai na Reuters ya ce daga 2011 zuwa 20215, kamfanoni masu zaman kansu a Amurka na dillancin gawa sun samu sassan jiki aƙalla 500,000, kuma sun rarraba sama da 182,000.
Makomar gawar mutum a koyarwa
Kusan duk wanda na yi magana da shi ya aminta cewa akwai buƙatar a tsaurara dokoki a Amurka game da dillancin gawa don riba.
Ms Schmitt ta Jami'ar California na ganin Amurka za ta iya bin sawun ƙasashen Turai wajen hana kasuwancin gawa.
Ta ce akwai 'yan kudaɗen da za a iya karɓa wajen sarrafa gawar - kamar wajen biyan kuɗin sufuri, ko kuma sinadaran da ake saka mata domin alkinta ta.
"Ba laifi idan kamfanoni sun karɓi kuɗi akan wannan. Amma maganar cewa a bar abin ya zama kasuwanci yakan sosa ran mutane. Yin hakan ina ganin yana saɓa wa imanin da masu bayar da gudumawar ke da shi na taimakawa waje koyar da ilimi."
Ta kuma bayar da shawarar cewa gwamnatin Amurka za ta iya kwaikwayon dokarta game da bayar da kyautar gaɓoɓi wajen haramta cinikayyar gawa.
A gefe guda kuma, akwai yiwuwar cigaban da ake samu na fasahar virtual reality (VR) - wato aiki a komfuta - za ta sa a daina buƙatar gawar mutum nan gaba. Ma'ana, mai ɗaukar horo zai iya zama a gaban komfuta kawai ya gwada aikin tiyata kan ƙirƙirarriyar gawa.
A 2023, jami'ar Case Western Reserve University ta zama na farko-farko a Amurka da suka daina amfani da gawar mutum wajen koyarwa, inda ta maye gurbinsu da na kwamfuta.











