Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas

USS Gerald R. Ford aircraft carrier

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Jirgin ruwan daukar jiragen yakin Amurka USS Gerald R. Ford ya nufi yankin Gabas ta Tsakiya

Amurka ta ce tana matsar da jiragen yakinta na ruwa da na sama zuwa yankin gabashin tekun mediteraniya sannan za ta bai wa Isra’ila karin kayan aiki da kuma na yaki.

Matakin na zuwa ne bayan harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila, lamarin da Shugaba Biden ya bayyana a matsayin “harin da ba a taba ganin irinsa ba kuma mai muni”.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka, ya ce akwai Amurkawa da aka kashe a harin.

Isra’ila ta ce an kashe mutum 700, yayin da aka yi garkuwa da mutum 100.

A Gaza, an kashe mutane fiye da 400 a hare-haren ramuwar gayya da Isra’ila ta kai ta sama, in ji hukumomin Falasdinawa.

Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin ya ce jirgin ruwan yaki na USS Gerald R Ford da ke dauke da makamai masu linzani da kuma wadansu manyan makamai guda hudu na kan hanyarsu ta zuwa yankin.

Sannan ya ce za kuma a aike da jiragen yaki.

Fadar White House ta ce sannan za a aika da karin taimakon soji zuwa Isra’ila, inda fadar ta ce za ta yi abin da ya dace domin kada makiya Isra’ila su ci karensu babu babbaka.

Aikewa da kayayyakin yaki alama ce da ke nuna cewa Amurka ta damu matuka cewa tashin hankali tsakanin Isra’ila da Hamas zai iya mamaye yankin.

Musamman, Amurka na kokarin ganin kungiyar Hezbollah ta Lebanon ba ta shiga yakin ba. Iran na goyon bayan Hezbollah kuma tana taimaka wa Hamas da kudi da makamai.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya nuna goyon bayansa kan harin da Hamas ta kai, inda ya ce Isra’ila ce ke da alhakin jefa yankin cikin hatsari.

Hamas ta ce tallafi daga Iran ya taimata wajen kai wannan harin wanda aka yi amfani da rokoki da jirage marasa matuka da kuma mayakan sa-kai da suka iya kutsawa cikin shingayen tsaro da Isra’ila ta yi a kewayen Zirin Gaza.

Sakataren wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce Amurka ba ta samu hujjar da ke nuna hannun Iran a harin ba, amma dai Iran ta jima tana taimako wa kungiyoyin da ke Gaza.

"Hamas ba za ta kasance Hamas ba, sai da taimakon da take samu daga Iran a tsawon shekaru. Ba mu ga hujja kai tsaye ta cewa Iran na da hannu a wannan harin ba. Amma ta dade tana taimakonsu," in ji Blinken.

A taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Iran ta musanta hannu a harin da aka kai wa Isra'ila.

Israila

Asalin hoton, Reuters

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daruruwan mutane sun bace. Daga cikinsu har da Ba'amurke dan Isra'ila, Hersh Golberg-Polin wanda ya halarci bikin kade-kade a hamadar da 'yan bindiga suka kai hari.

Iyayensa sun shaida wa jaridar Jerusalem Post cewa sun samu sakonni guda biyu daga wajensa inda ya rubuta: "Ina sonku" da kuma "Ku yi hakuri".

Rahotanni sun ce akwai Amurkawa da dama da suka bace, ciki har da wata 'yar fafutuka Vivian Silver.

Wata kawar matar 'yar shekara 75 ta shaida wa jaridar Canadian Jewish News cewa Misis Silver ta kira ta, inda ta bayyana mata cewa mayakan Falasdinawa suna bakin kofarta.

"Na ji kara da ihu inda Vivian ke fada da su kafin wayar ta tsinke," in ji ta.

Jakadan Isra'ila a Amurka, Micheal Herzog ya shaida wa CBS News cewa akwai Amurkawa cikin sojoji da fararen hula da aka yi garkuwa da su a kudancin Isra'ila, amma bai yi wani karin bayani ba.

Amurka tana bai wa Isra'ila tallafin biliyoyin dala na taimakon soji duk shekara.

Tun daga Yakin Duniya na biyu, Isra'ila ce ta fi kowacce kasa samun tallafi daga Amurka.

Nan ba da jimawa ba, kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gana a New York domin tattaunawa kan tashin hankali a Isra'ila da Gaza.