Za a riƙa fallasa sunayen waɗanda suka zubar da shara barkatai a Japan

Japan

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ga wanda bai saba ba, rarrabe shara domin zubar da ita bisa tsari a Japan wani abu ne mai matuƙar wahala - a ƙasar wadda ta zama mai tsauraran sharuɗɗan zubar da shara.

To yanzu a birnin Fukushima, da alama lamarin zai ƙara tsauri.

Farawa daga watan Maris mai zuwa, ma'aikata za su zaƙulo ƙunshi-ƙunshi na shara waɗanda aka zubar ba bisa ƙa'ida ba - kamar waɗanda ba a rarrabe su yadda ya kamata ba, ko waɗanda suka tumbatsa fiye da ƙa'ida - daga nan a sanar da al'ummar gari sunayen masu su.

Sabuwar dokar wadda ta samu amincewar shugabannin hukumar kula da birnin a ranar Talata, na zuwa ne a daidai lokacin da Japan ke ƙoƙarin inganta harkar zubar da shara a ƙasar.

Yayin da hukumomi a birane da dama na Japan suka amince da a riƙa bincika ledojin shara domin gano kantunan ba su tsara sharar da suka fitar yadda ya kamata ba, Fukushima na cikin birane na farko-farko da suka amince a fallasa ɗaiɗaikun mutane baya ga kantuna da masana'antu.

A cikin sanarwar da suka tura wa BBC, Hukumar rage bazuwar bola ta Fukushima ta ce rashin tsara shara kafina zubar ya ƙara yawan yadda ake samun shara na watsewa a cikin birnin wanda ya haifar da yaɗuwar tsuntsaye masu cin ƙazanta.

"Rashin zubar da shara yadda ya kamata babban abin damuwa ne kasancewar yana kawo lalacewar muhalli," in sanarwar.

"Saboda haka nan muna ɗaukan batun zubar da shara bisa tsari a matsayin abu mai muhimmanci."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A shekarar da ta gabata, an bayar da rahoto sama da 9,000 game da saɓa ƙa'idar zubar da shara.

Yanzu, a maimakon kwashe sharar da aka zubar yadda bai kamara ba, ma'aikatan kwashe shara na Fukushima kan liƙa takarda a jikin ledar shara da aka ajiye a ƙofar gida domin sanar da mai ita cewa bai bi ƙa'ida ba, wanda hakan ke sawa dole sai mai ita ya mayar da sharar cikin gida ya rarrabe ta yadda ya kamata sannan ya sake fito da ita.

A sabuwar dokar Fukushima, duk mutumin da ya kasa rarrabe shara yadda ya kamata kafin fito da ita ƙofar gida, zai samu gargaɗin baka daga ma'aikata, idan bai gyara ba za a tura masa da takardar gargaɗi.

Idan kuma duk da haka bai gyara ba, to za a ɗauki sunansa a wallafa a shafin intanet na gwamnati.

A Japan kowane birni na da ƙa'idarsa ta kwashe shara.

A Fukushima, doka ta tanadi cewa dole ne a ajiye ledojin shara a wasu wurare da aka tanada kafin ƙrfe 8:30 na safe, kuma ba za a ajiye su su kwana a wurin ba.

Akan rarrabe sharar ne ta yadda za a ƙunshe waɗanda za a sake sarrafawa daban, wadda za a watsar daban sai kuma wadda ba ta ruɓewa daban.