Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɓangarori biyar da gwamnati ta gaza kare fararen hula a Najeriya - Rahoto
Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Human Rights Watch ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza wajen kare rayukan fararen hula a ƙasar.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a rahoton da ta fitar kan abubuwan da suka faru a shekarar 2025, wanda ta fitar a watan Fabrairun bana.
Ƙungiyar ta ce matsalar tsaro ta ƙaru a faɗin Najeriya, wanda ta ce ya ƙara nuna rashin ƙoƙarin hukumomin ƙasar wajen kare rayukan al'umma.
Rahoton ya ƙara da cewa an samu hare-hare masu muni na Boko Haram a jihar Borno, wanda a cewarta yake nufin ayyukan mayaƙan kungiyoyin Boko Haram da Iswap sun sake kazancewa. Rahoton ya kuma ce ana ci gaba da kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin kasar ta Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai ta sha bayyana cewa tama bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin.
A ɗaya ɓangare kuma, rahoton ya zargi jami'an tsaron ƙasar da take hakkin ɗan-adam a ƙoƙarin daƙile matsalolin, ciki har da harin sojojin ta sama da ya yi ajalin mutane.
Sannan ta ce ana ci gaba da fuskantar daɗaɗden rikicin manoma da makiyaya a yankin arewa ta tsakiyar kasar.
Garkuwa da mutum 2,938 a arewa maso yamma
A rahoton ƙungiyar, ta ce an ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, amma kuma hukumomin ƙasar sun gaza wajen daƙile matsalar.
"A rahoton cibiyar tattara bayanan sirri ta SBM Intelligence, ta gano an yi garkuwa da aƙalla mutum 2,938 a arewa maso yamma tsakanin watan Yulin 2024 zuwa watan Yunin 2025, wanda shi ne kusan kashi 60 na sace-sacen mutane da aka yi a ƙasar."
Ƙungiyar ta ce rahoton ya ƙara da cewa Zamfara ce kan gaba a wannan bangare, inda aka yi garkuwa da aƙalla mutum 1,203, sai Kaduna ke biye mata da mutum 629, sai Katsina mai 566, sai kuma jihar Sokoto da aka sace mutum 358.
Da take zayyana wasu daga cikin hare-haren da suka fi illa, rahoton ya ambato harin da aka kai a ranar 19 ga Agustan bara a wani masallaci a ƙauyen Unguwar Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda aka kashe masallata 32.
"Duk da hukumomi sun yi alƙawarin ɗaukar mataki, amma har yanzu babu wani gamsasshen bayani kan yunƙurin da ake yi na bincike ko kama waɗanda ake zargi, ballanta a musu hukunci."
Haka kuma rahoton ya ƙara da cewa rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 52 a watan Afrilu, sannan ya raba kusan mutum 2,000 da muhallansu a ƙauyuka shida na ƙaramar hukumar Bokkos na jihar Filato.
"Sannan a watan Yuni wasu mahara sun kashe mutum 59 a garin Yelewata da ke ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benue, kamar yadda hukumomi suka sanar, amma mutanen gari suka ce waɗanda aka kashe sun haura 100."
Rahoton ya ce duk da cewa hukumomi sun sanar da kama mutum 53, ciki har da 26 da ake zargi da hannu a kisan Yelewata, "har yanzu babu labarin waɗanda suka yi kisan Bokkos."
Ƙungiyar ta ƙara da cewa a tsakanin 18 zuwa 21 ga Nuwamba, an sace ɗaruruwan mata ƴan makaranta a jihohin Kebbi da Neja, inda ta ce duk da an ceto su, gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin Tinubu ba ta bayyana asalin waɗanda suka sace ɗaliban ba.
"Babu cikakken bayani kan bincike ko kame ballantana ma hukunta waɗanda ake zargi da laifi. Hukumomin Najeriya sun gaza ɗaukar darasi wajen daƙile irin waɗannan hare-haren," a cewar rahoton.
Hare-haren Boko Haram
Rahoton ya ƙara da cewa hare-haren Boko Haram da Iswap kan fararen hula sun ƙaru.
Rahoto ya bayyana cewa a watan Mayun bara an kashe kusan mutum 57, sannan aƙalla mutum 70 suka ɓace bayan mayaƙan sun kai hari a ƙauyukan Mallam Karamti da Kwatandashi a ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Haka ƙungiyar ta ce a watan Satumba, maharan sun kai hari a Darul Jamal a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, inda rahotanni suka ce an kashe aƙalla mutum 60, ciki har da sojoji.
Haka kuma rahoton ya bayyana hare-haren ƴanbindiga a yankin kudu maso gabas, waɗanda ƙungiyar ta ce suna da alaƙa da ƙungiyoyin ƴan awaren IPOB.
Ƙugiyar Amnesty ta ruwaito cewa a watan Mayu, wasu mahara da ake zargi ƴan IPOB ne sun kashe aƙalla mutum 30 a babbar hanyar Okigwe-Owerri zuwa Iamo, duk da cewa IPOB ta musanta zargin.
Rahotanni sun ƙara da cewa yawancin lokuta, hukumomi suna gazawa wajen kamawa da hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Tauye haƙƙin fararen hula daga jami'an tsaro
A watan Agusta, jami'an tsaro sun kama Omoyele Sowore bisa zargin shi da laifukan intanet, inda ya yi zargin cewa ƴansanda sun zalunce shi, amma rundunar ƴansanda ta musanta zargin.
Rahoton ya ƙara da cewa a watan Janairun, sojojin saman Najeriya sun kai wani hari da suka ce na kuskure a Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Maradun na jihar Zamfara, inda suka kashe aƙalla mutum 20, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Sojojin sun ce sun kai harin ne kan ƴanbindiga, sannan suka sanar da cewa za su bincika zargin kashe fararen hula, amma har yanzu babu cikakken bayani kan binciken.
Haƙƙin furta albarkacin baki
Haka kuma rahoton ya ƙara da cewa an kama tare da tsare ƴan jarida da masu amfani da kafofin sadarwa da dama, inda suke amfani da dokar laifukan intanet.
Rahoton ya ambato kama lauya Dele Farotimi da Nurudden Adegbenro Adenekan da Buhari Olanrewaju Ahmed da Saidu Musa Tsaragi da sauran su.
Rahoton ya ƙara da cewa ko a watan Fabrairu, majalisar Birtaniyya ta amince da buƙatar a gaggauta sakin mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu bayan yanke masa hukuncin kisa da daina amfani da hukuncin kisa baki ɗaya a ƙasar.
Sai dai duk da cewa kundin mulkin Najeriya ya bayar da ƴancin furta albarkacin baki, ɓatanci laifi ne babba.
Haƙƙin mata da masu lalurar nakasa
A watan Janairu, cibiyar Initiative for Equal Rights (TIERs) ta ruwaito lokuta 556 da aka kama ko gabatar da aƙalla mutum 850 da suke da alaƙa da fafutikar ƴancin jinsi wato LGBT a jihohi 29.
Rahotanni sun nuna cin zarafi da ɓata suna da neman na goro da ƙarfi da yaji da sauran su.
A watan Mayun bara ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da sake duba dokar haramta cin zarafin mutane, wanda aka yi domin ingantawa da bayar da daƙile cin zarafin mutane saboda bambancin jinsi.
Haka kuma rahoton ya nuna cewa masu buƙata ta musamman sun fuskanci wariya, wanda ke jefa su damuwa a ƙasar, duk da haramta nuna musu bambanci da aka yi a ƙasar a shekarar 2021.