An yi waje da Tottenham daga Champions League

Tottenham ta yi rashin nasara a hannun AC Milan da ci 0-0 a wasa na biyu a Champions League da suka kara ranar Laraba a Ingila.

Tottenham ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Cristian Romero jan kati saura mint 12 a tashi daga wasan.

AC Milan ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe da cin 1-0 gida da waje, bayan da ta yi nasarar cin 1-0 a wasan farko a Italiya cikin watan Fabrairu.

Antonio Conte ne ya ja ragamar wasan a Ingila, wanda ya yi jinya a Italiya tun daga wasan da Milan ta ci 1-0 cikin watan Fabrairu.

Wasa na shida kenan da suka fafata a tsakaninsu, inda kowacce ta ci biyu da canjaras biyu kenan.

Tottenham ta kara fadawa cikin kalubale, wadda kungiyar da ke buga Championship ta fitar da ita daga FA Cup na kakar nan.

A karshen mako Wolverhampton ta yi nasara a kan Tottenham, wadda ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai ranar Laraba a Ingila.

Ba ta samu lashe Carabao Cup ba, wanda Manchester United ta dauka a karon farko karkashin Erik ten Hag, bayan nasara a kan Newcastle United.

Yanzu Tottenham za ta mayar da hankali kan wasan Premier ko ta kare cikin 'yan hudun farko a kakar nan.

Yanzu tana mataki na hudu a kan teburi da maki 45 da tazarar maki uku tsakaninta da Liverpool ta biyar.

Ranar Asabar Tottenham za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a gasar Premier League.