Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan cire Maryam Shetty daga jerin ministoci

Asalin hoton, FACEBOOK/MARYAM SHETTY
Kamar yadda aka tafka muhawara lokacin da sunanta ya bayyana a cikin waɗanda shugaban ƙasa ya gabatar wa majalisa, haka nan aka sake buɗe wata sabuwar muhawarar bayan cire sunan nata.
Za a iya cewa kusan dukkanin matakan biyu sun zo da mamaki.
Tun farko dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunan Maryam Ibrahim Shettima, a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za a naɗa minista daga jihar Kano.
Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da haka a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aika wa majalisar kuma ya karanta yayin wani zama a Juma'ar nan.
Ba a dai bayyana dalilin janye sunan Maryam Shetty a jerin ministocin da Tinubun zai naɗa ba.
Hotuna da suka riƙa yawo a shafukan sada zumunta sun nuna Maryam Shetty a harabar Majalisar Dokokin Tarayya a safiyar Juma'a domin tantancewa.
Rahotanni sun ce a wannan lokacin ne ta samu labarin an maye gurbinta da wasu sunayen biyu, wato Festus Keyamo da kuma Dr. Mariya Mairiga.
Muhawara ta kaure
Bayan ɓullar labarin cire sunan Shetty, sai aka kaure da muhawara a fili da kuma shafukan sada zumunta.
Kamar yadda aka samu mabanbantan ra'ayoyi lokacin da aka bayyana sunanta, haka nan ma aka riƙa samun ra'ayoyi masu karo da juna bayan cire sunanta.
Sai dai an samu mutane da dama waɗanda suka taya ta alhini kan faruwar lamarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A shafin tuwita, tsohon mai bai wa tsohon shugaban ƙasa shawara kan sadarwa @BashirAhmaad cewa ya yi "A kodayaushe ina sha'awar jajircewar Maryam Shetty wajen yi wa al'umma hidima, kuma ƙwarewarta ba abin tantama ba ce. Duk da cewa wannan lamari kamar abin takaici ne, na yi amannar cewa juriya da jajircewarta za su yi mata jagora wajen samun sabbin hanyoyi mafiya kyawu da za su kawo kyakkyawan tasiri. Allah ya sa haka ne mafi alheri."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
A shafin tuwita @gimbakakanda ya ce "Maryam Shetty jajirtacciyar mai biyayya ga jam'iyya ce. Matakin maye gurbinta ba ya da alaƙa ko kaɗan da ce-ce-ku-cen da ake yi. Yana iya yiwuwa wannan sauyi ya zama abin da ya fi gare ta, kuma muna mata fatan alheri a rayuwarta ta gaba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Haka nan ma @dawisu cewa ya yi "Na tausaya wa Maryam Shetty, koda ta cancanta ko ba ta cancanta ta zama minister ba. Ina ɗora laifin a kan hanyar da aka bi wajen sakawa da kuma cire sunanta. Wannan abin kunya ne, kuma zai iya zama abin da ba za ta taɓa warwarewa daga gare shi ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Shi ma @Maxajee ya ce "Tsaya, wane labari nake ji cewa an cire Maryam Shetty daga jerin sunayen ministoci?
Wannan abin ya yi banbarakwai. Me ya sa za su sanya sunanta tun farko? Ban san me ya sa suke yi mata haka ba, kuma ya lafiyar ƙwaƙwalwarta abu ne da ya kamata a martaba."
Wace ce Mariya Mahmud Bunkure?
Mariya Mahmud Bunkure ita ce wadda ta maye gurbin Maryam Shetti a matsayin wadda za a naɗa minista daga jihar Kano.
Dr Bunkure ta yi karatu a makarantar sakandare ta Foundation Secondary School da ke Kano.
Ta kuma karanta harkar likitanci a jami'ar Bayero da ke Kano, kuma ɗaya ce daga cikin kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.