Iyaye a Afghanistan kan bai wa 'ya'yansu maganin barci saboda yunwa

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
- Marubuci, Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Afghanistan correspondent
"Watanni biyu da suka wuce ne lokaci na ƙarshe da na samu damar sayen madarar jaririya ta. Kullum sai in cika kwalbar da shayi. Ko kuma in jiƙa burodi a shayi sannan in ciyar da ita," in ji Sohaila Niyazi, wanda ke zaune kasan gidanta na laka da ke saman sama wani tudu a gabashin Kabul.
Babu hanyoyin zuwa gidanta - dole sai an bi ta wata hanya ta cikin laka wadda ke da magudanar bahaya a gefenta.
Sohaila bazawara ce. Tana da ‘ya’ya shida, autarta ‘yar wata 15 ce mai suna Husna Fakeeri. Shayi da Sohaila ke nuni da shi shi ne abin da ake yawan sha a ƙasar Afganistan, wanda ake yi da koren ganye da ruwan zafi, ba tare da madara ko sukari ba. Ba ya ƙunshe da wani sinadirin gina jiki ga jaririyarta.
Sohaila na daya daga cikin mutum miliyan 10 da suka daina samun tallafin abinci na gaggawa daga shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) a shekarar da ta gabata - sakamakon karancin kuɗaɗe. Abu ne mai muni, musamman ga kimanin gidaje miliyan biyu da mata ke tafiyar da su a Afganistan.
A ƙarƙashin mulkin Taliban, Sohaila ta ce ba za ta iya fita aiki don ta ciyar da iyalinta ba.
“Akwai dararen da ba mu da abin da za mu ci, na ce wa yarana, ina zan je bara a wannan lokaci da dare? Suna kwana cikin yunwa, idan sun farka sai na yi tunanin abin da zan yi. Idan makwabtanmu suka kawo mana abinci, yaran sukan yi ta wawaso, suna cewa 'ba ni, a ba ni'. Ina kokarin raba shi a tsakaninsu domin kwantar masu da hankali," in ji Sohaila.
Don kwantar ma jaririyarta da hankali, Sohaila ta ce ta kan ba ta "maganin barci".
"Na kan ba ta ne don kada ta farka ta nemi madara saboda ba ni da madaran da zan ba ta, bayan na ba ta maganin ta kan kwana ta na barci," in ji Sohaila. "Wani lokaci ina dubawa ko tana raye ko ta mutu."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mun yi tambaya game da maganin da take ba 'yarta sai muka gano cewa sanannen maganin ƙan-jiki ne. Barci na ɗaya daga cikin abubuwan da maganin ke haifarwa.
Likitoci sun shaida mana cewa, duk da cewa ba shi da lahani fiye da suran magungunan kwantar da hankali da kuma na rage damuwa da wasu iyaye a Afganistan ke bai wa 'ya'yansu da ke fama da yunwa, shan maganin da yawa na iya haifar da matsalolin nimfashi.
Sohaila ta ce mijinta farar hula ne da aka kashe a wata arangama da aka yi a lardin Panjshir a shekarar 2022, a faɗa tsakanin dakarun Taliban da masu adawa da mulkin Taliban. Bayan rasuwarsa, ta dogara ne kan taimakon gari, da mai da wake da shirin WFP ke bayarwa.
Yanzu shirin WFP ta ce tana iya samar da kayayyaki ga mutane miliyan uku kacal - ƙasa da kashi huɗu na waɗanda ke fama da matsananciyar yunwa.
Sohaila ta dogara kacokan akan gudummawar dangi ko makwabta.
Tsawon lokacin da muke can, jaririyar, Husna tayi shiru kuma bata wata hidima.

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
Tana fama da rashin abinci mai gina jiki, ta kasance ɗaya daga cikin yara sama da miliyan uku da ke fama da matsalar a ƙasar, a cewar Unicef. Fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na waɗannan suna da mafi munin nau'insa - matsanancin rashin abinci mai gina jiki. Wannan shi ne mafi muni da aka taba fuskanta a Afghanistan, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
Kuma yayin da rashin abinci mai gina jiki ke addabaR ƙananan yara a ƙasar, an janye tallafin da ya hana tsarin kiwon lafiyan ƙasar rugujewa.
Ƙungiyar agajin ƙasa da ƙasa ta Red Cross na biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya, tare da ba da tallafin magunguna da abinci a asibitoci sama da 30 - wani matakin gaggawa na wucin-gadi da aka aiwatar bayan sauyin gwamnati a shekarar 2021.
Yanzu ba ta da kuɗaɗen da za ta ci gaba, kuma an janye tallafi daga yawancin cibiyoyin kiwon lafiya, ciki har da asibitin yara ɗaya tilo na Afganistan, asibitin Indira Gandhi da ke birnin Kabul.
''Yanzu gwamnati ce ke biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya. An kuma yanke kusan rabin albashinsu'' in ji Dr Mohammad Iqbal Sadiq daraktan kula da lafiya da Taliban ta nada a asibitin.
Asibitin ta kuma rufe sashen ta na majinyatan jeka-ka-dawo inda ta ke kula da waɗanda ke buƙatar a kwantar da su a asibitin ne kadai.
Sashen tamowar asibitin a a cike ya ke maƙil, wasu lokutan sukan ajiye fiye da yaro ɗaya a kan gado.
A gefe guda Sumayya na zaune. Duk da cewa watan ta 14 da haihuwa nauyinta bai wuce na sabon jaririn da aka haifa yanzu ba. Fuskarta duk ta yi tamoji kamar ta tsohuwar mace.
Kusa da ita akwai Mohammad Shafi. Ya na da rabin nauyin da a kamata a ce yana na shi a watanni 18 da haihuwa. Mahaifinsa mayaƙin Taliban ne, wanda ya mutu a hatsarin mota. Mahaifiyarsa kuma ta rasu sakamakon rashin lafiya.
Lokacin da muka wuce gefen gadonsa tsohuwar kakarsa Hayat Bibi ta nufo mu a gigice tana neman bayar da labarinta.

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
Ta ce 'yan Taliban sun taimaka wajen kawo jikanta asibiti, amma ba ta san yadda za su cigaba da rayuwa ba.
"Na dogara da rahamar Allah, babu inda zan koma, gaba ɗaya a rikice na ke" Hayat Bibi ta ce yayin da idanunta suka cika da hawaye. "Ni ma fama da kai na na ke yi, kai na yayi zafi ina ji kamar zai fashe."
Mun tambayi babban mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ko me suke yi don shawo kan ƙasashen duniya su ba da ƙarin taimako.
"An yanke taimakon ne saboda tattalin arzikin ƙasashen masu ba da taimako ba ya tafiya yadda ya kamata. Kuma an samu manyan bala'o'i guda biyu - annobar korona da yakin Ukraine. Don haka ba za mu iya tsammanin taimako daga gare su ba. Ba za mu sami taimako ta hanyar tattaunawa da su ba.” inji shi.
"Dole ne mu zama masu dogaro da kai. Tattalin arzikinmu ya daidaita kuma muna bayar da kwangilolin haƙar ma'adinai wanda zai samar da dubunnan guraben ayyukan yi. Amma ban ce a daina bayar da agaji ba saboda har yanzu muna da fuskantar ƙalubale.
Shin ya gane cewa manufofin Taliban sun taimaka wurin ta'azara matsalar; cewa masu ba da gudummawa ba sa son ba da kuɗi ga ƙasar da gwamnati ta sanya takunkumi mai tsauri akan mata?
"Idan har ana amfani da taimako a matsayin matakin matsin lamba to Masarautar ta Musulunci tana da nata dabi'u da za ta kiyaye ko ta halin ƙaƙa. 'Yan Afganistan sun yi babbar sadaukarwa a baya don kare kimarmu kuma za su jure yanke taimakon," Mista Mujahid yace.
Kalamansa ba za su yi wa 'yan Afganistan dadi ba. Kashi biyu bisa uku na mutanen ƙasar ba su san inda za su ci abinci na gaba ba.
A wani gida mai ɗaki ɗaya a Kabul, mun haɗu da wata mata da ta ce 'yan Taliban sun hana ta sayar da 'ya'yan itatuwa da kayan lambu, da safa da sauran abubuwa a kan titi. Ta ce an taɓa tsare ta sau ɗaya. An kashe mijinta a lokacin yaƙin kuma tana da ’ya’ya huɗu da ta ke kula da su. Ba ta son a bayyana sunan ta.
Ta fashe da kuka jim kaɗan bayan fara bayani kan halin da ta ke ciki.
“Ya kamata a kalla su bari mu yi aiki mu samu abin dogaro da kai, na rantse da Allah ba za mu fita yin munanan abubuwa ba. Muna fita nemo wa ‘ya’yanmu abinci ne kawai, suna takura mana haka,” inji ta.

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
Yanzu an tilasta mata aika ɗanta mai shekaru 12 zuwa wurin aiki.
"Na tambayi wani ɗan uwana a Taliban, me zan ciyar da 'ya'yana idan ba na samun kuɗi? Ya ce a ba su guba amma kada ku fito daga gidajenku," in ji ta. "Sau biyu gwamnatin Taliban ta ba ni wasu kuɗaɗe, amma ba su kai ko ina ba."
Gabanin Taliban ta ƙwace iko, kashi uku cikin huɗu na kuɗaɗen da jama'a ke kashewa sun fito ne daga kuɗaɗen kasashen waje da aka bai wa gwamnatin da ta gabata kai-tsaye. An dakatar da shi a watan Agustan 2021, hakan ya tura tattalin arzikin ƙasar cikin wani mummunan yanayi.
Hukumomin agaji sun shigo don samar da tallafi na wucin-gadi.
An dakatar da mafi yawan wannan tallafin a halin yanzu.
Yana da wuya a iya kwatanta munin wannan lamarin. Mun sha gani akai-akai a wannan shekarar da ta gabata.
Miliyoyin mutane suna rayuwa ta hanyar cin busasshen burodi da ruwa.
Da yawa ba za su kai labari cikin lokacin sanyi ba.










