APC ta shiga gaban PDP a sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo

Yayin da ke ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba, manyan jam'iyyun siyasar jihar biyu na ci gaba da yin kankankan.
Shugaban Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Minna, Farfesa Farouk Adamu Kuta ne babban jami'i tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Babbar Jami’ar INEC ta ƙasa da ke kula da zaɓen, Farefesa Rhoda Gumus ta ce a halin yanzu akwai sakamakon ƙananan hukumomi 14 zuwa 15 a zauren tattara sakamakon.
Kawo yanzu an bayyana sakamakon ƙananan hukumomi 16, yayin da sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta samu ƙananan hukumomi biyar, inda ta lashe ƙananan hukumomi huɗu daga ciki, inda APC lashe ƙananan hukumomi 11 daga ciki.
Ga sakamakon kamar haka:
Ƙaramar hukumar Igueben
APC- 5907
PDP - 8470
Ƙaramar hukumar Esan ta Yamma
APC - 12952
PDP - 11004
Ƙaramar hukumar Owan ta Yamma
APC - 12277
PDP - 11284
Ƙaramar hukumar Uhunmwonde
APC - 8776
PDP - 9339
Ƙaramar hukumar Ovia ta Arewa maso
APC - 13225
PDP - 15311
Ƙaramar hukumar Esan ta Kudu maso
APC - 8398
PDP - 14199
Ƙaramar hukumar Egor
APC - 16760
PDP - 14658
Ƙaramar hukumar Akoko-Edo
APC - 34847
PDP - 15865
Ƙaramar hukumar Esan ta Tsakiya
APC - 10990
PDP - 8618
Ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas
APC - 10648
PDP - 12522
Ƙaramar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma
APC - 10150
PDP - 10260

Ƙaramar hukumar Orhionmwon
APC - 16059
PDP - 14614
Ƙaramar hukumar Owan ga gabas
APC - 19380
PDP - 14189
Ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas
APC - 20167
PDP - 9683
Ƙaramar hukumar Etsako ta Tsakiya
APC - 11906
PDP - 8455
Ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma
APC - 32107
PDP - 17483
Kawo yanzu jam'iyyar APC ta bai wa PDP tazara da kaso 10 cikin 100 na ƙuri'un da aka tattara

Za mu ci gaba da sabunta muku wannan labari yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon ƙarin ƙananan hukumomi











