Cocin Najeriya ya gabatar da addu'o'i ga Sarauniya Elizabeth II

Ɗaruruwan mutane ne suka taru a Cocin Najeriya na ɗariƙr Anhalica don gabatar da addu'o'i na musamman na tuna wa da Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
An yi taron addu'o;in ne a cocin da ke Abuja, babban birnin Najeriyar, a ranar Alhamis 15 ga watan Satumban 2022.
Rabaran Dr Henry Ndukuba, wanda shi ne babban Archbishop kuma mai kula da cocin ne ya shirya taron addu'o'in.
Shi ma wani babban jami'in cocin, Rabaran Ali Buba Lamido, wanda kuma shi ne shugaban cocin reshen jihar Kaduna, ya ce "Dariƙar Angalican ta samo asali ne daga Cocin Ingila kuma a tarihi Sarki ko Sarauniyar Ingila ne ke shugabantar cocin.
"Ita ce shugabar cocinmu kafin rasuwarta don haka ne muke tuna ta da girmama ta ta hanyar yin wannan taron addu'o'in, mu kuma haƙurƙurtar da kawunanmu," in ji shi.
Jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing da mataimakinta Matt Munroe, duk sun halarci taron addu'o'in.
A wajen taron sun yabi rayuwar Sarauniyar, sun yi mata addu'ar samun dacewa sannan suka yi wa Sarki Charles addu'ar samun nasara a mulkinsa.










