Abin da ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin Dogara da Wike

Dogara da Wike
Bayanan hoto, Dogara ya koma PDP ne bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da APC

A Najeriya, ce-ce-ku-ce ya ɓarke tsakanin wasu manyan 'yan siyasar ƙasar a jam'iyyar PDP, bayan wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun fice daga jam'iyyar zuwa babbar jam'iyyar hamayyar.

Mutanen, waɗanda suka haɗar da tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawan sun yi ƙorafin cewar ba za su goyi bayan takarar musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ke yi ba, lamarain ya da ya suka fice daga jam'iyyar.

To sai dai tun bayan ficewar tasu kawunansu suka fara rarrabuwa game da jam'iyyar da za su koma inda wasu ke ganin jam'iyyar Labour ce ta dace da su, a yayin da wasu suka koma jam'iyyar PDP.

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara na daga cikin waɗanda suka koma jam'iyyar PDP, kuma bangaren dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, lamarin da bai yi wa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike daɗi ba.

Gwamnan ya ce ya yi mamaki yadda Dogara - wanda a baya ke iƙirarin cewa ya kamata mulki ya koma kudancin ƙasar indai ana son zaman lafiya da adalci - a yanzu kuma yake mara wa Atiku baya.

A wani taron ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar ranar Litinin Wike ya ce ya yi mamaki yadda wasu da suka shigo jam'iyyar a 'yan kwanaki nan, har suka samu zarafin yin magana game da jam'iyyar tasu.

Ya ƙara da cewa Dogara da Babachir sun ziyarce shi kuma sun cimma yarjejeniyoyi, inda kuma ya zargi Dogara da rashin mutunta yarjejeniyar da suka cimma.

''Ba za ka iya faɗar abu, kuma ka tsaya a kansa ba''?, tambyar da Wike ya yi wa Dogara ke nan.

Gwamnan ya kuma ce ba zai yadda da mutanen da ba sa mutunta yarjejeniya ba.

Sai dai a jerin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Litinin , tsohon kakakin majalisar wakilan ƙasar Yakubu Dogara ya ce ya yi mamakin yadda Wike ya kasa tuna ainihin abin da suka tattauna, suka amince a yarjejeniyar tasu.

“Zuwa ga ɗan uwana Gwaman Nyesom Wike; ban taɓa tunanin cewa cutar mantuwa na daga cikin abubuwan da ke damunka ba,'' kamar yadda ya rubuta a a shafinsa na Tuwita.

“Me ya sa kake tunanin cewa kai ƙaɗai ne kake da damar karya kowacce irin yarjejeniya da aka ƙulla da kai''?

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

''Me tattaunawa da yarjejeniyar tamu ta ƙunsa. Me yasa sai ɓangarenka kawai za a yi wa biyayya a yarjejeniyar''?

Dogara ya ce shi ba ya cin amanar aboki ko ɗan uwa ba, lamarin da ya ce shi ya sa ba zai mayar wa Wike martani na gidan talbijin ba.

Ya ce zai ci gaba da sirrinta yarjejeniyar da suka ƙulla da Wike ba zai bayyana wa duniya ba.

Haka kuma ya ƙalubalanci Wike da cewa idan yana ganin babu wata matsala game da bayyana wa duniya abinda suka ƙulla to ya ba shi a rubuce.

''Zan ci gaba da sirrinta yarjejeniyarmu, amma idan kana ganin babu damuwa na bayyana wa duniya, to ka ba ni a rubuce, ni kuma zan bayyana wa mutane su kuma su yi alƙalanci kan waye ya faɗi gaskiya tsakanina da kai. Na ma gode wa Allah akwai shaidu lokacin yarjejeiyar tamu''.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Jam’iyyar PDP dai ta shiga cikin ruɗani ne tun bayan zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa da ta gudanar, inda Atiku Abubakar ya yi nasara a kan sauran masu neman jam’iyyar ta tsayar da su takara ciki har da Gwamna Wike.

Lamarin da Wike da wasu abokansa suka fusata saboda a cewarsu hakan ya saɓa da yarjejeniyar jam'iyyar inda suka yi ta kiraye-kirayen shugaban jam'iyyar na ƙasa Iyorchia Ayu da ya sauka daga muƙaminsa.

Wannan dambarwa ta raba kan 'ya'yan jam'iyyar inda wasu gwamnonin jam'iyya suka ware tare da kafa ƙungiyar gwamnoni ta G5, waɗanda ƙarara ke nuna adawa da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar tasu.