Ban yi watsi da Wike ba, na dauki mutumin da zan iya aiki da shi ne -Atiku Abubakar

Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce ya ki daukar Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a matsayin mataimakinsa ne saboda yana son ya dauki mutumin da zai "ji dadin aiki da shi”.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a hira ta musamman da ya yi da gidan talbijin na Arise TV ranar Juma'a.
Dan takarar na PDP ya dauki gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023, duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya ba shi shawarar daukar Wike.
Rashin daukar Wike ya jawo ce-ce-ku-ce da tayar da jijiyoyin wuya a cikin jam'iyyar inda wasu suka rika hasashen cewa gwamnan na Jihar Ribas ka iya ficewa daga cikinta.
Hasalima wasu jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban, cikinsu har da gwamnonin APC da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Kwankwaso, na cikin wadanda suka kai wa Wike ziyara a birnin Fatakwal inda suka yi zawarcinsa.
Sai dai jam'iyyar PDP ta nada kwamitin da zai rarrashe shi ya ci gaba da zama a cikinta, inda shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar, Sanata Walid Jibrin, ya shaida wa BBC Hausa cewa idan ta kama za su durkusa wa Gwamna Wike domin hana shi fita daga cikinta.
Da yake magana game da matakin da ya dauka na zabar mataimakinsa, Atiku ya ce ya dauki Okowa maimakon Wike ne saboda yana son mutumin zai iya “gabatar da tsare-tsaren jam'iyyarmu, kuma wanda zai iya hada kan 'yan kasa”.
“Ban yi watsi da Gwamna Wike ba. Babu wanda aka yi watsi da shi a jam'iyya. Amma dole ka fahimci cewa hurumin dan takara ne ya zabi mataimakinsa — mutumin da ya yi amannar cewa zai yi aiki da shi cikin lumana, kuma wanda zai gabatar da manufofin jam'iyya, kuma ya yi kokarin hada kan kasa,” in ji Atiku.

Asalin hoton, OTHER
Ya kara da cewa: “Gwamna Wike dan siyasa ne mai basira. Yana da karfin hali da juriya. Na yi amannar cewa yana da makoma a game da harkokin siyasar kasar nan. Wannan batu ba na yin watsi da shi ba ne. Tabbas ba haka ba ne. Ina ganin ya yi matukar tsauri a ce mun yi watsi da Gwamna Wike. Tabbas ba haka ba ne.”











