Dalilin hatsaniya kan man fetur tsakanin Kenya da Uganda

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Basillioh Rukanga
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
Hatsaniya ta ɓarke tsakanin Kenya da maƙwabciyarta Uganda game da cinikin man fetur, inda shugaban Uganda ke cewa "ƙwari" sun "cuce" shi.
Tsawon shekaru, Kenya ta sha sayo mai daga waje kuma ta sayar wa maƙociyar tata a gabashin Afirka - amma damarta ta ƙasar da ta fi sayar da man a yankin na cikin haɗari.
Hatsaniyar ta fara ne a farkon watan nan lokacin dqa Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya zargi dillalan mai na Kenya da ƙara farashinsa da kashi 58 cikin 100, abin da ya jawo wa ƙasarsa "babbar asara".
Ya kuma soki "ƙwarin cikin gida" game da "cutar" Uganda da suka yi ta hanyar ƙin ɗaukar mataki da suka yi bayan farashin man ya fara tashi a farkon shekarar nan.
Uganda ta shafe shekaru tana sayo kashi 90 cikin 100 na man fetur daga Kenya, wanda take sayar wa kamfanonin ƙasarta - sauran kuma ta sayo daga Tanzania.
Gwamnatin Mista Museveni ta ce tana son ƙarin 'yanci game da harkar saye da sayar da makamashin man fetur.
"Kenya ta daɗe tana tsara wa Kenya na'uin man fetur ɗin da za ta saya, da lokacin da za ta saya, da yadda za ta saya, da yawansa, da kuma farashinsa," kamar yadda Ministar Makamashi ta Uganda Ruth Nankabirwa ta bayyana.
Amma kuma 'yan kasuwar makamashi na Kenya sun zargi gwamnatin Kenya game da tashin farashin man.
A baya, akan tallata damar shigo da man fetur ga kamfanonin Kenya. Duk kamfanin da ya yi nasara a neman shi ne zai shigo da shi a madadin sauran. Tsari ne na biyan iya abin da aka shigo da shi, wanda ake biya da dalar Amurka.

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma a watan Maris, gwamnatin Kenya ta shiga lamarin saboda ƙarancin dalar Amurka, abin da ya jawo wahalhalu ga kamfanonin da ke sayo kayayyaki daga waje saboda yadda bankuna ke ƙayyade adadin dalolin.
Sai gwamnatin ta ɗauki matakin yin ciniki kai-tsaye da kamfanonin ƙasashen waje masu sayar da man kan lamuni ga 'yan kasuwar cikin gida da kuma masu yin safararsa daga Kenyan zuwa waje.
Hakan na nufin za a jinkirta biyan kuɗin duk yarjejeniyar da aka ƙulla da tsawon wata shida.
A ƙarƙshin yarjejeniyar, kwastomomi a Kenya za su sayi man da kuɗin ƙasar na shiling, amma kwastomomin ƙasar waje za su biya da dala.
Akan adana kuɗin a wani asusun banki mai yawan kuɗin-ruwa tsawon wata shida kafin a gama biyan kuɗin - abin da ke ɗan rage yawan ƙarancin dalar.
John Njogu, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar mai a Kenya, ya faɗa wa BBC cewa Uganda ta yi daidai da ta ƙi yarda da tsarin saboda ita ba ta fama da ƙarancin dalar kuma bai kamata ta biya ƙari a farashin man ba.
Yanzu da Uganda ke son ficewa daga cinikin, Kenya za ta ƙara shiga matsala game da ƙarancin dala - yayin da Mista Njogu ke cewa Uganda kan biya dala miliyan 180 duk wata ga kamfanonin Kenya.
Shi ma jagoran adawa a Kenya Raila Odinga ya soki yarjejeniyar, wanda ya bayyana shi da "babbar zamba".
Ya yi kira ga hukumar yaƙi da rashawa ta Ethics and Anti-Corruption Commission (EACC) ta yi bincike game da abin da yarjejeniyar ta ƙunsa, wanda ya ce ya kamata a faɗa wa 'yan ƙasa.
"Dillalan da Shugaban Uganda Museveni ke magana a kai su ne jami'an gwamnatin Kenya," a cewarsa.
Amma Ministan Makamashi na Kenya Davis Chirchir ya kare yarjejeniyar lamunin, inda ya faɗa wa 'yan majalisa cewa ta taimaka wajen hana hauhawar farashin mai.
Wannan cecekuce ya yi daidai da wata badaƙala da ke faruwa a Kenya game da tan 100,000 na man fetur da aka shiga da shi mai darajar dala miliyan 110 - inda ake rigima kan wanda ya mallake shi kuma yanzu lamarin na kotu.
Lauyan wata 'yar kasuwa da ke cikin badaƙalar ya yi zargin cewa wasu da ke son "sace" kayan sun yi garkuwa da ita tsawon kwanaki.
Gwamnatin Kenya ta musanta hannunta a lamarin kuma ta ce kamfaninta ba shi da lasisi.
Ba 'yan Kenya da shugaban Uganda ne kaɗai ke nuna ɓacin rai ba. Ƙasashen Burundi, da Dimokuraɗiyyar Kongo, da Rwanda, da Sudan ta Kudu duka na sayen wani ɓangare na fetur ɗinsu daga Kenya.
"Yankin ya shiga ruɗani," in ji Dzombo Mbaru, shugaban kamfanin Kenya mai suna Mardin Energy, a hirarsa da BBC.
Ya ce ba wai sabuwar yarjejeniyar ce kawai ke da matsala ba, yana nufin harajin mai da ake karɓa ma na da matsala kuma yana buƙatar "sake lale".

Asalin hoton, Reuters
Uganda ta ce ta ƙulla yarjejeniya da Vitol Bahrain wajen ɗaukar nauyin aikin samar da man fetur ɗinta. Ta kuma ce za ta dinga adana man a Tanzania.
Yayin da Uganda ke shirin fara samar da mai da kuma gina matatar man, za ta iya "samar da albarkatun mai da za su yi gogayya, wanda babu wasu dillalai" cikin 'yan shekaru ga Gabashin Afirka.
Mista Njogu na ganin yunƙurin Uganda abu ne da ake buƙata a Kenya game da harkar shiga da fetur: "Muna buƙatar sauyi kan yadda muke gudanar da kasuwanci."
Amma dai babban darasi ne da zai shafi tattalin arzikin Kenya nan da shekaru masu zuwa, a cewarsa.










