'Gargaɗin da Amurka ta yi kan Najeriya ya saɓa ka'ida'

fg

Asalin hoton, Muhammad Idris Malagi

Gwamnatin Najeriya ta ce gargadin da ofishin jakadancin kasar Amurka ya yi a karshen makon da ya gabata cewa Amurkawa su lura da otal-otal din da za su zauna domin samun yiwuwar kai hare-hare, abu ne mai tayar da hankali da ka iya shafar tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin Najeriyan, ta bayyana hakan ne ta bakin ministan yada labarai, Alhaji Muhammad Idris, wanda ya ce babu abin da hakan zai haifar sai tsananin fargaba ga kowa.

Yayin tattaunawarsa da BBC a taron manema labaran da ya gabatar domin mayar da martani ga wannan gargaɗi da Amurka ta yi, Ministan ya ce irin wannan mataki ya saɓawa tsarin diflomasiyya tsakanin ƙasashe.

"Duk lokacin da aka ce Amurka ko wata ƙasa ta Turai ta yi irin magana irin wannan yakan kawo fargaba, mutane sai su tsorota kai idan kana Abuja aka ce ka da ka je wani waje sai ka yi ta mamaki ka tambaya menene ke faruwa,' in ji Ministan.

Ya ƙara da cewa ba aifi ba ne don sun shaida wa mutanensu abin da suka gani, amma ya kamata Amurka ta yi takatsantsan don kada su jefa mu cikin ruɗani.

Waɗannan kalamai suka janyo aka tambayi Minista Muhammad Idris, hakan na nufin Amurka ba ta tuntuɓi Najeriya ba? sai ya ce "To gaskiya ba su tuntube mu ba.

"Ba sa tuntuɓa, suna dai amfani ne da abin da suke gani a gabansu sai su yi irin wannan bayani. In da Sun tuntuɓe mu da mun ba su shawara akan yadda za su yi," kamar yadda ya bayyana.

Ministan ya amsa cewa babu shakka akwai wuraren da ake fuskantar matsalar tsaro a Abuja, amma ba ko ina ba.

Kuma ya ce ba su taɓa "rufa-rufa" kan hakan ba.

Ministan yada labaran ya yi kira ma su amfani da shafukan sada zumunta da su zama masu kishin ƙasa da kuma yaɗa labaran gaskiya.

A cewarsa irin labaran da suke bayarwa na da tasiri game da irin mataki da Amurka ta ɗauka a yanzu.

Ya kuma nemi haɗin kan masu amfani da shafukan sada zumunta da su zama masu kishi da yunƙurin da ciyar da Najeriya gaba.