'Muna bincike kan zargin rashin bai wa sojojinmu isasshen abinci'

Asalin hoton, Taoreed Lagbaja/Twitter
Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ce "za ta gudanar da bincike nan take a kan ƙorafe-ƙorafen" rashin bai wa sojoji da ke yaƙi da Boko Haram isasshen abinci.
Hedkwatar sojojin ƙasan ta ce hankalinta ya kai kan ƙorafe-ƙorafen cewa dakarunta da ke fagen yaƙi da Boko Haram, ba sa samun ingantaccen abinci.
Wani sojan Najeriya da muka zanta da shi ta wayar tarho daga arewa maso gabashin Najeriya, inda suke yaƙi da 'yan Boko Haram, ya ce matsalar rashin ingantaccen abinci da suke ciki, da wuya a iya misalta ta.
“Mun sha fita zuwa daji, ba tare da mun ci wani abin kirki ba. Matsaloli da muke fuskanta ba su da adadi,” in ji sojan wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Ya yi zargin cewa abincin da ake ba su bai taka kara ya karya ba, kafin su fita bakin fama.
Sai dai a cikin sanarwa da mai magana da yawunta, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar ranar Talata, rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike nan take a kan zarge-zargen domin gano haƙikanin gaskiyar abubuwan da ke faruwa.
Sanarwar ta ambato babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja na cewa: “Muna son tabbatarwa dukkan dakarunmu da kuma al’umma cewa za mu yi cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Shi dai sojan da muka zanta da shi ya bayyana mana cewa: “Akwai rundunoni daban-daban a inda muke (aiki), wataƙila abin da ake ba mu a wajen da muke, ba haka yake a sauran wurare ba.
"Wani lokaci akan mutum ya ci abincin da ake dafawa, gwara an ba ka naira ɗari biyu ka sayi burodi ko cincin,” in ji shi.
“Teba ake dafa mana mu ci, idan za mu fita aiki. Wani lokacin ma sai garin ya lalace. Ta yaya za a ba ka wannan abinci sannan a ce ka je ka yi yaƙi da Boko Haram?”
"Ci-kar-ka-mutu kawai ake ba mu"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewarsa “Idan ka ga soja ya ci abincin da ake dafawa, to ya ci ne kawai don kar ya mutu”.
“Nama guda biyu ake saka mana, wanda shi ma ɗan ƙanƙani ne."
Ya ƙara da cewa sau tari, ana caccanza musu abinci a tsakanin teba da shinkafa da kuma tuwo da ake ba su sau uku a rana. Ya ce yawan abincin da ake ba su, ba ya isarsu har su ci, su ƙoshi.
“Idan ka ga na ci abincin da aka girka, to nama kaɗai nake ɗauka, amma ko yaushe ka zo ɗakina, za ka samu abincin da nake dafawa da kaina.
Ya ce: “Da safe, ana ba mu burodin da bai fi naira ɗari ba, da burbuɗin madara da bonvita, ba sukari ko ganyen shayi a ciki.
“Daga nan ba za mu sake cin komai ba, sai misalin ƙarfe 2 na rana."
Ya ce idan suka fita daji don yin samame, ba za su sake cin komai ba a tsawon lokacin, sai sun koma sansani.
Rundunar sojin ƙasa dai ta ce mai yiwuwa ne akwai inda ake samun matsala nan da can, kuma a shirye take domin shawo kan lamarin.
Ta ce tana bai wa dakarunta abinci ne bisa wani tsari da take aiki da shi don tabbatar da ganin dukkan dakarunta, musamman ma waɗanda ke fagen daga, na samun isasshen abinci mai gina jiki, kuma ana dafa musu abincin ne da inganci.
“Tuni muka fara gudanar da binciken cikin gida kan hanyar da abincin yake bi, domin isa ga dakarun, da ingancin abincin da kuma sauran abubuwa da suka janyo aka kai ga wannan lamari," in ji sanarwar.
A cewarta, tana gudanar da komai a fayyace don tabbatar da gaskiya da adalci, kuma ba za ta lamunci sakaci ba.
Kuma duk wanda aka samu da laifi, za a hukunta shi yadda doka ta tanada, in ji rundunar sojin ƙasan Najeriya.











