'Sai hukumomin tsaro sun haɗa kai a ga bayan matsalar tsaron Najeriya'

Asalin hoton, OTHERS
Wasu daga cikin ƴan majalisar dattawan Najeriya, sun bayyana cewar matukar ana son samun nasarar magance matsalolin ‘yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta sai an samu hadin kai a tsakanin hukumomin tsaron kasar.
Sanata Ɗan-dutse Muntari Muhammad, mai wakiltar Katsina ta Kudu a majasalisar dattijan ta Najeriya, shi ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.
Sanatan ya ce matsalar tsaro da, samar da ayyukan yi ga matasan kasar, na daga cikin matakan da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita a jihohi irin na su.
Ya ce a tattaunawar da suka yi a majalisa sun duba yadda za a fuskanci matsalar tsaron ta Najeriya da idon basira.
Haka kuma ya ce kasar na bukatar addu'a da goyon bayan kowa da kowa, yadda za a samu cigaba kasa ta zamo ingantatta.
Alhaji Muntari ya ce dole ne sai hukumomin tsaro sun hada kai suna tuntubar juna da yin abu tare.
''Sannan ya kasance ana daukar matakai na bai daya a tsakanin jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi da Katsina da Kaduna da Niger don a kawo kasar,'' in ji shi.
Ya ce, ''Idan ba haka ba idan ana yakarsu a Zamfara sai su koma wata jihar, to wannan yana cikin matsalar ya kamata jami'an tsaron su sauya.''
''Kana ya kasance ana zuwa duk inda maharan nan suke ana farmakinsu,'' in ji shi.
Ya kara da cewa madamar ba a zuwa a yake su to akwai matsala.
Sanatan ya ce za su so a ce an bullo da tsaron da za a yi wa maharan afuwa su fahimci cewa kisan mutane da kuma karbar kudi ba zai dore ba,''wannan karya ce,'' ya ce.
Ya ce ''ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, kuma muna ganin yadda wasu kasashen suka fada matsaloli iri-iri, da na tattalin arzikin da na tsaro, na zamasn lafiya, inda ake yaki muna gani, don haka mutane su sa tsoron Allah a duk abin da za su yi domin a kawo wa kasar cigaba da nasarorin da aka sa a gaba.''











