Man Utd na son Dibling da Rigg, PSG ta ɗaukaka ƙara kan Mbappe

Tyler Dibling

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na sha'awar matashin ɗan wasan gaba na gefe na Southampton Tyler Dibling ɗan Ingila mai shekara 18 to amma ƙungiyarsa na son ya ci gaba da zama. (GiveMeSport)

Bayern Munich ta haƙura da neman tsawaita kwantiragin Alphonso Davies, yayin da Real Madrid ke sha'awar ɗan bayan na Kanada mai shekara 23. (Relevo)

Napoli da Inter Milan na sha'awar ɗan bayan Arsenal da Japan Takehiro Tomiyasu, mai shekara 25. (Calciomercato )

Kociyan AC Milan Paulo Fonseca, wanda ƙungiyarsa za ta kara da abokan hamayya Inter Milan ranar Lahadi ya ce shi ba ya tunani a kan raɗe-raɗin da ake yi game da makomarsa bayan da ƙungiyar ta fara kakar bana da rashin abin a zo a gani. (Football Italia)

Kociyan Liverpool Arne Slot ya ce, ƙungiyar ta manta da maganar kasa ɗauko ɗan wasan tsakiya na Sifaniya, Martin Zubimendi mai shekara 25 daga Real Sociedad a bazara. (Mirror)

To amma kuma Liverpool ɗin na ci gaba da maganar kwantiragin ɗan wasan gaba na gefe na Kolombiya Luis Diaz mai shekara 27, duk da saɓanin da suka samu da wakilin ɗan wasan mai shekara 27 a bazara. (Teamtalk)

Mai tsaron ragar Espanyol Joan Garcia ya ce ko kaɗan sha'awarsa da Arsenal ke yi ba ta ɗauke masa hankali ba a bazara, duk da cewa wataƙila Gunners za su iya sake nemansa ɗan wasan na Sifaniya mai shekara 23 a lokacin kasuwar sayar da 'yan wasa ta watan Janairu. (Mirror)

Tauraron ɗan wasan Lyon Rayan Cherki na shirin ƙulla sabon kwanriragi da ƙungiyar har zuwa 2027, duk da cewa ana danganta shi da Liverpool, da Tottenham da kuma Paris St-Germain. (Foot Mercato)

Paris St-Germain ta ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da aka yi mata na cewa ta biya Kylian Mbappe, mai shekara 25 - wanda ya koma Real Madrid a bazaran nan - fam miliyan 46 na albashi da kuɗaɗen alawus-alawus da ta rike masa lokacin yana ƙungiyar. (Athletic)

Newcastle United za ta kori darektan wasanninta Paul Mitchellkafin ta yanke shawarar korar kociyanta Eddie Howe idan saɓanin da ke tsakanin mutranen biyu ya ci gaba. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya na Sunderland Chris Rigg, mai shekara 17, wani matashin ɗan wasan ne da Manchester United ke so kuma ƙungiyar ta Old Trafford na kallon matashin na Ingila a matsayin wani sabon Jude Bellingham'. (HITC)

Tsohon kociyan Barcelona Xavi ya ce ya samu gayyata mai kyau daga ƙungiyoyoyi to amma ya ce bai shirya komawa fagen haorad da 'yan wasa ba. (Revelo)