Barcelona ta ci wasa na bakwai a jere da fara La Liga a bana

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Getafe 1-0 ranar Laraba wasan mako na bakwai.

Robert Lewandowski ne ya ci ƙwallon kuma na bakwai a kakar nan shi ne kan gaba a yawan zurawa a raga mai bakwai, sai Raphinha mai biyar.

Kenan Lewandowski ya zama ɗan kasar Poland mafi cin ƙwallaye a La Liga, mai 49 a raga, Jan Urban na biye da shi mai 48 a tarihi.

Wannan shi ne karo na uku da Barcelona ke fara kakar La Liga da tagomashi, karo na biyu da fara nasara bakwai da fara gasar a jere, bayan bajintar da ta yi a 2013/14 karkashin Tata Martino.

Getafe ba ta taɓa zuwa ta doke Barcelona a gida ba a karawa 20 da ta je, wadda ba ta ci wasa ko ɗaya ba a kakar nan.

Haka kuma ƙwallo uku Getafe ta zura a raga, idan aka kwatanta da 23 da Barcelona ta ci daga fafatawa bakwai a La Liga.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya da maki21 daga wasa bakwai da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.

Wasannin da ke gaban Barcelona nan gaba:

Liga Asabar 28 ga watan Satumba

  • Osasuna da Barcelona

Champions League Talata 1 ga watan Oktoba

  • Barcelona da Young Boys

Liga Lahadi 6 ga watan Oktoba

  • Alaves da Barcelona

Liga Lahadi 20 ga watan Oktoba

  • Barcelona da Sevilla

Champions League Laraba 23 ga watan Oktoba

  • Barcelona da Bayern Munich

Liga Lahadi 27 ga watan Oktoba

  • Real Madrid da Barcelona