Uefa na neman filin da zai karɓi wasan karshe a Champions League 2027

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa na neman flin da zai shirya wasan karshe a Champions League a 2027, bayan da ta karɓe daga Milan.
Tun farko an tsara San Siro ne zai karɓi bakunci daga baya aka janye, bayan da mahukuntan Milan suka kasa fayyace ko gyare-gyaren filin ba zai shafi gasar ba.
AC Milan da Inter Milan na duba yiwuwar gina sabon filin wasa a San Siro, hakan ne ya sa Uefa ke tsoron kada haka ya kawo tsaiko ga Champions League.
Ana sa ran sanar da wadda za a bai wa baƙuncin wasan karshe a Champions League na 2027 a watan Mayu ko Yunin 2025.
An yanke wannan hukuncin a babban taron Uefa ranar Talata, an kuma cimma matsaya can sauye-sauye da aka samu wajen samar da kuɗin shirya gasar.
Manyan gasa biyar ta Turai - Premier League da La Liga da Ligue 1 da Serie A da kuma Bundesliga - sun amince da biyan kuɗin haɗin gwiwa kan Yuro miliyan 10 kwatankwacin (£8.3m) a kowace kakar har zuwa 2026-27.
An samu karin Yuro miliyan 1.5, kenan za su raba fam miliyan 256.3 mai makon fam miliyan 147.4.






