Trump na fuskantar Turjiya daga Jordan kan shirin kwashe al'ummar Gaza

    • Marubuci, Lucy Williamson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
    • Aiko rahoto daga, Jordan
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ana sa ran Donald Trump ka iya fuskantar matukar turjiya daga Sarki Abdallah na Jorda a fadar White House a Yau, a yayin zaman ganawarsu na farko da shugaban na Amurka, tun bayan da Trump din ya nemi a mayar da al'ummar Gaza zuwa Jordan.

Jordan, babbar kawar Amurka, na tsaka mai wuya, na goyan bayan Falasdinawa a gida, ko tallafin da take samu daga Amurka na soji da harkokin diflomasiyya daga wajen Amurka.

Wadannan matsaloli, tuni suka nuna sakamakon gwaji a yakin da aka fuskanta a Gaza, inda ake kokarin amfani da wannan salo, da shirin Trump ke neman tarwatsa zaman lafiya a Gaza.

Ya fadada bukatarsa na cewar a mayar da al'ummar Gaza zuwa Jordan ko Masar, inda yake sanar da kafar yada labarai ta Fox cewar ba su da yancin da za su koma gida, wani da idan aka aiwatar da shi, ya ci karo da dokar kasa da kasa.

A ranar Litinin ne, ya ce zai tsayar da ayyukan jinkai ga Jordan da Masar, idan har ba su amince da karbar Falasdinawa da za a kai musu don zaman hijira ba.

Wasu daga cikin masu zazzafar adawa da mayar da al'ummar Gaza zuwa Jordan, su ne mutanen na Gaza da aka taba mayar da su can.

Mutum 45, 000 da ke zaune a cikin halin matsi, kusa da birnin Jerash da ke arewacin Jordan, Falasdinawa yan gudun hijira na zune a nan.

wani karfe ne ke sakale a jikin wata kofar shiga wani dan karamin shago, yayin da yara ke ta sagaraftu akan jakkai a tsakanin rumfunan kasuwar.

Iyalai masu yada ke nan, asalinsu yan Gaza ne: daga Jabalia, Rafah, Beit Hanoun. Da yawa daga cikin su, sun bar gida ne tun yakin Larabawa da Isra'ila, inda suka sami matsuguni na wucin gadi. Bayan gwammon shekaru, har yanzu suna zaune a nan.

"Donald Trump mutum ne mai girman kai, ne da son kansa,"Maher Azazi mai shekaru 60 ya fada mun. "Yana da irin tunanin mutanen da, irin tunain nan na masu yan kasuwar da."

Maher ya bar Jabalai a matsayin yaro karami. har yanzu wasu daga cikin danginsa na chan. yanzu suna chan suna tonan gidan su da aka rusa musu, yayin da har yanzu ake neman gawar wasu yan uwansa 18 da baa san inda suke ba.

Duk da matsanacin halin da ake fuskanta a chan, Mr Azazi ya ce mutanen Gaza sun koyi darasi, na magabata, wanda kuma "inda yanzu sun gwamace, su fada cikin teku da su bar garinsu."

Wadan da suke ganin barin Gaza, a matsayin hanyar zaman hijira na wucin gadi, yanzu sun gane yanzu cewar suna taimakawa Isra'ilawa masu tsatsauran ra'ayi da ke son kwace filayen Falasdinu.

"Mu yan Gaza mun taba shiga wannan hali a baya" a cewar Yousef, wanda aka haife shi a sansanin yan gudun hijira. " A baya, sun shaida mana cewar zaman na wucin gadi ne, za mu ko ma gida. Sai dai har yanzu ba mu ga hakan ba.

"Lokacin da magabatan mu suka tafi, ba su da makaman da za su yi fada, kamar yadda Hamas ke da su," wani mutum ya shaida mun. "Yanzu zamanin matasa ne, da ke sane da irin abubuwan da ya faru da magabatan mu, wanda hakan ba zai kuma faruwa ba. Yanzu akwai turjiya."

Falasdinawa dai ba su kadai ba ne, za su yi hijira zuwa Joardan ba, wadda ke zagaye da rikice-rikicenn da aka fuskanta a Gabas ta tsakiya.

Iraqiyawa da suka tserewa yakin da aka yi a kasar tun 2000, su ma sun tsero zuwa nan. Bayan wasu shekaru su ma yan Syria suma sun zo, wanda hakan ya harzuka sarkin Jordan ya yi wani gargadi cewar kasar ta fi "fuskantar mastala".

Yan asalin kasar ta Jordan sun dora alhakin kwararowar yan gudun hijirar zuwa kasar, kan dimbin rashin aikin yi da talauci da suke fama da shi a gida. wata gidauniyar rarraba abinci na babban masallacin Amman ya sahida mana cewar kimanin mutum 1, 000 ne ke karbar abinci a wajen su a kullum.

Yayin da ya ke jiran aiki a wajen wani masallaci, mun hadu da Imad Abdallah da abokinsa Hassan, dukkan su leburori ne , da suka jima ba su yi aiki ba.

Halin da ake ciki a Jordan a baya sai sam barka, amma da aka fara yaki a Iraq, abubuwa sun tabarbare, lokacin da ake yakin a Syria, lamarin ya tsanata, yanzu gashi ana yaki a Gaza, lamarun sun kara tabrbarewa, "a cewar Hassan. "Yake-yaken dukkan wani yaki da ke faruwa a kusa da mu, mu kan zama wadan abin ke karewa a kai, saboda kasar mu kasa ce da ke taimakon mutane."

Imad ya damu ne da yadda zai ciyar da iyalinsa, da yaransa hudu.

"Yan kasar wajen sun zo, suna karbe aikin mu" ya fada mun. Yanzu wata na 4 babu aiki. Ba ni da kudi, babu abinci. Idan yan Gaza suka zo mutuwa zan yi.

Amma Jordan na fuskantar mastin lamba, daga kwayen ta da ke bata agajin Soji. Tuni Trumo ya dakatar da tallafin Amurka da ya kai dala biliyan 1.5 a shekara. Inda ake ci gaba da hasashen ci gaba da fsukantar tankiya tsakanin sabon shugaban Amurka da shugaban siyasa, da ke turjiya.

Jawad Anani, tsohon mataimakin Firai minista ne da ke da kusanci da gwamantin Jordan, ya ce Sarki Abdallah zai aikawa Trump sako, a ranar Talata, wanda zai futo da komai karara: "Za mu duba dukkan wani yunkuri daga Isra'ila, ko wasu, da ke yukurin korar mutane daga gidajensu a Gaza da Yamma da gabar kogin Jordan, wanda hakan babban laifi ne karara. Amma dukkan wani yunkuri, na trusasawa mutanen barin gidajensu, ba komai zai haifar ba illa kaddamar da barkewar yaki."

Ko da al'ummar Gaza sun so yin hijirar da kashin kawunansu, na wucin gadi, a wani shirin fadada Gabas ta tsakiya, ya ce babu yardar ko kadan a ciki.

"Babu wani karfin guiwa, "a cewarsa. "In dai Netanyahu na ciki, da shi da gwamantinsa, babu karfin guwai, na cikar alkawarurukan da kowa ke yi. Fakat."

Aniyar Trump na ganin Gaza ta koma karkashin ikon babbar 'yar lelenta, ka iya samun nasara.

A ranar juma'ar da ta gabata, dubban mutane ne suka yi zanga zanga kan bukatar ta Trump.

Jordan ta kasance sansanin sojin Amurka, yayin da miliyoyin yan hijira, da sauran ayyukanta na tsaro na da matukar mahimmanci ga Isra'ila, baya ga damuwa da hanyoyin da ake fasa kauri, zuwa gabas ta tsakiya.

Dukkan wani yunkuri na, haifar da rashin zaman lafiya a Jordan, barazana ne ga kawayenta. idan kuwa zaman lafiya shi ne karfin jordan, akwai barazanar fuskantar rikicin, shi ne babban abin da makami, kuma abin kariyarta.