Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa matan Koriya ta Kudu ba sa samun haihuwa?
- Marubuci, Jean Mackenzie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
- Aiko rahoto daga, Seoul
A wata ranar Talata, Yejin na girka wa ƙawayenta abinci a gidanta da ke wajen birnin Seoul, inda take zaune ita kaɗai ba tare da abokan zama ba.
A yayin da suke tsaka da cin abincin, ɗaya daga cikin ƙawayen nata ta kunna wata manhajar katun a wayarta, inda nan take katun ɗin ya ce ''ku yi a hankali, kada ku mutu ku kaɗai kamar mu''.
Sai dukkansu suka ƙyalƙyale da dariya.
"Abin dariya ne, amma abin akwai firgitarwa. Saboda mun san mu ne ke haddasa wa kanmu mutuwa cikin kaɗaici,'' in ji Yejin mai shekara 30 wadda mai shirya shirin talbijin ce.
Daga ita har ƙawayen nata babu wanda ke wani shiri na samun 'ya'ya. Suna cikin gungun matan da ke da aƙidar rashin son haihuwa a ƙasar.
Koriya ta Kudu ce ƙasa mafi karancin haihuwa a duniya, kuma adadin haihuwar a kullum na ci gaba da raguwa, inda ya kai matakin da bai taɓa kai wa ba cikin wannan shekara.
Alƙaluman da hukumomi suka fitar a ranar Laraba, sun nuna cewa an samu ƙarin raguwar haihuwa da kashi takwas a shekarar 2023 zuwa 0.72.
Wannan shi ne adadin yaran da ake sa ran mata za su haifa a tsawon rayuwarsu. Idan ana so al'ummar ƙasar ƙaru sosai, ya kamata a ce adadin ya kai kashi 2.1
Idan wannan abu ya ci gaba, ana hasashen cewa adadin al'ummar zai ragu da rabi zuwa shekarar 2100.
'Babbar barazana ga ƙasa'
A duniya, ƙasashen da suka ci gaba na samun raguwar haihuwa, to sai dai babu ƙasar da ta kai Koriya Kudu samun raguwar.
Hasashen ya tayar da hankali.
Nan da shekara 50 masu zuwa, adadin ma'aikata a ƙasar za su ragu zuwa rabi, mutanen da ya kamata su ja ragamar rundunar sojin ƙasar za su ragu da kashi 58, kuma kusan rabin al'ummar ƙasar za su zama tsoffi masu shekaru sama da 65 a duniya.
Wannan mummunar makoma ce ga tattalin arzikin ƙasar da tsaro da ci gaban ƙasar, lamarin da ya sa 'yan siyasar ƙasar suka ayyana batun da ''wata babbar barazana ga ƙasar''.
Kusan shekara 20 da suka wuce gwamnatocin ƙasar sun yi ta zuba maƙudan kuɗaɗe da suka kai dala biliyan 286 don magace matsalar.
Ma'auratan da suka haifi 'ya'ya kan samu kyautar kuɗaɗe, a kowane wata tare da rage musu kuɗin hayar gidaje, da ɗaukar su a mota kyauta, da magunguna kyauta a asibiti.
To amma duka waɗannan dabaru ba su yi aiki ba, lamarin da ya sa 'yan siyasa suka riƙa tunanin wasu sabbin hanyoyin dabarun jan hankalin mutanen ƙasar domin su amince su riƙa haihuwa.
Dabarun da aka ɓullo da su sun haɗa da ɗauko masu reno daga ƙasashen Kudu maso gabashin Asiya tare da biyan su kudin da bai kai mafi ƙarancin albashi ba a ƙasar, tare da hana maza shiga aikin sojin ƙasar idan ba su da aƙalla 'ya'ya uku kafin su kai shekara 30.
Sai dai wani abin mamaki, shi ne akan zargi mahukunta da rashin sauraron buƙatun mutane, musamman mata.
Mun kwashe kusan shekara guda muna zagayawa cikin ƙasar inda muka tuntuɓi mata masu yawa dangane da dalilinsu na rashin son haihuwa.
A lokacin da Yejin ta kai shekaru 20 da haihuwa ne ta yanke shawarar rayuwa ita kaɗai, ta bijire wa al'adun ƙasar, inda ake kallon zaman kaɗaici a matsayin wani baƙon al'amari a al'adun ƙasar.
Shekara biyar da suka gabata ne, ta yanke hukuncin rayuwa ba tare da yin aure da kuma haihuwa ba.
"Samun saurayi abu ne mai wahala a Koriya, haka ma wanda zai aure ka da wanda zai kula da 'ya'yan da za ka haifa,'' kamar yadda ta faɗa.
A shekara 2022, kashi biyu cikin 100 ne kawai na haihuwar da aka samu a Koriya ta Kudu aka haifa ba tare da aure ba.
'Yadda ake daɗewa a wurin aiki'
A maimakon haka, Yejin ta zaɓi ta mayar da hankalinta kan aikinta na gidan talabijin, wanda ta ce ba zai ba ta damar kula da jariri ba. An dai son Koriy ta Kudu da tsawon lokutan aiki.
Yejin kan yi aiki daga ƙarfe 9 na safe zuwa 6 na maraice, to amma ta ce a lokuta da dama ba ta barin ofis sai ƙarfe 8 na dare, a wasu lokuta ma fin haka.
Idan ta koma gida babu abin da ya rage mata in ban da share gidanta ko ta motsa jiki kafin ta kwanta barci.
"Ina son aikina, ina samun rufin asiri daga gare shi, amma aiki a Koriya na da wahala, wurin aikin kan zama tafkar gidanka, saboda yadda kake daɗewa a wurin'', in ji ta.
'Na san abubuwa da dama'
Wata mata mais hekara 28 da ke aiki a hukumar kula da yawan ma'aikata, ta ce tana ganin mutanen dole suka bar ayyukansu, ko suka kasa cin jarrabawar ƙarin girma, daga tafiya hutun haihuwa, wanda hakan ne ya sanya ta ɗaukar matakin kada da haihu.
Ma'aikata maza ta mata na da hutun shekara guda cikin shekara takwas na farko na rayuwar 'ya'yansu.
Amma a 2022, kashi 7 ne kawai na iyaye maza suka yi amfani da hutunsu, idan aka kwakwanta da kashi 70 na iyaye mata.
Matan Koriya ta Kudu na karatu mai zurfi idan aka kwatanta da na sauran ƙasashen yankin, amma duk da haka ƙasar na da wagegen giɓin albashi tsakanin maza da mata, kuma mafi yawan matan ƙasar ba sa aiki, idan aka kwatantan da maza.
Mun haɗu da Stella Shin bayan tashi daga makaranta, inda take koyar da ƙananan yara.
"Kalli yaran nan don Allah. Abin burgewa," in ji malamar makarantar. Amma a yanzu da take shekara 39, Stella ba ta da 'ya'ya, ba mataki ba ne da na zaɓar wa kaina, in ji ta.
Ta yi aure shekara shida da suka gabata, kuma duka ita da mijin nata na son samun haihuwa, to amma aiki ya hana su fuskantar auren nasu, a yanzu ta ce ta yarda yanayi rayuwarsu ne ya sa hana su samun haihuwa.
"Iyayen mata na buƙatar ajiye aiki na kusan shekara biyu domin kula da 'ya'yansu, kuma wannan zai sanya min damuwa'', in ji ta.
''Ina son aikina tare da kula da kaina''.
Fiye da rabin al'ummar Koriya ta Kudu na rayuwa ne a Seoul babban birnin ƙasar, inda a nan ne aka fi samun ayyukan yi.
Stella da mijinta sun yi ƙoƙairn ficewa daga birnin Seoul zuwa wasu larduna, sai dai har yanzu ba su iya sayen gida ba.
Adadin yaran da aka haifa a birnin Seoul ya ragu zuwa kashi 0.55, adadi mafi ƙanƙanta a ƙasar.
Sannan akwai tsadar makarantu masu zaman kansu. yayin da tsadar gidaje ta kasance matsala ce ta ƙasa, amma a wannan fannin Koriya ta yi fice.
Daga shekara hudu, akan kai yara azuzuwan koyar da lissafi da turanci zuwa na kiɗa da Taekwondo.
Wani bincike da aka yi a 2022, kashi biyu cikin 100 na iyaye ba sa iya biyan makarantu masu zaman kansu, yayin da kashi 94 ke cewa nauyi ne hakan.
A matsayin malamain a ɗaya daga cikin makarantun, Stella ta fahimci halin da ake ciki sosai.
Tana ganin yadda iyaye ke kashe kimanin dala 890 kowanne wata a kan yaro guda, wasu da yawansu ba sa iya biyan hakan.
Wata matsalar al'umma
A birnin Daejon, abin da Jungyeon Chun ta kira ''ita ƙadai take lura da 'ya'yansu". Bayan ɗauko yarinyarta mai shekara bakwai da kuma ɗanta mai shekara hudu daga makaranta, tana ya da zango a wajen wani wasan yara inda take kwashe awanni har sai mijinta ya dawo daga wajen aiki. Kuma mawuyaci ne ya koma gida a lokacin barci.
"Ina jin cewa ban ɗauki matakin da ya dace ba wajen haihuwar yaran nan, na yi tsammanin zan iya komawa aiki cikin gaggawa a ƙanƙanin lokaci," in ji ta.
Amma ba jimawa sai matsalolin kuɗin suka danno kai, kuma anan ne ta gano ita kadai ce take raino. Mijinta da ke kasuwanci da kuma harkar ƙungiyoyi baya taimaka mata da rainon yara ko ayyukan gida.
"Ina fusata ko da yaushe," in ji ta. "Na yi ilimi sosai, kuma an kuma koya min cewa mata da maza babu banbanci, domin haka ni ba zan ci gaba da amincewa da hakan ba."
Wannan shi ne ƙirjin matsalar
Sama da shekara 50 da suka gabata, tattalin arzikin Korea na samun ci gaba cikin gaggawa, abin da ya sanya mata zuwa karatu a manyan makarantu da kuma samun ayyuka, abin da yake ƙara girmama burikansu, sai dai matakin mata da uwa ba sa samun ci gaba kamar hakan.
Jungyeon wadda take a fusace, ta fara bibiyar yadda wasu iyaye mata ke lamuransu. "Sai na riƙa lura da ƙawayen nawa su ke tsallakar da yaransu titi, abin takaici, kusan ko ina haka matsalar take."
Ta fara tattara bayananta tana wallafawa a intanet. "Nan da nan aka fara ba ni labarai iri-iri," a cewarta. Nan da nan sai shafinta ya yi fice, tsakanin matan da ke da alaƙa da aikinta a faɗin ƙasar, yanzu kuma Jungyeon ta rubuta littatafan ban dariya guda uku.
Tace yanzu ta share doguwar hanya cikin damuwa da nadama. "Na yi burin sanin yadda ake rainon yara, da abubuwan da ake tsammanin iyaye mata su yi," kamar yadda ta bayyana.
"Akwai matan da ba su da yara yanzu, saboda suna da kwarin gwiwar yin magana akai."
Yanzu Jungyeon cikin ɓacin rai take ko da yaushe, ta na cewa ana hana mata damarsu ta zama iyaye, saboda tashin hankalin da yanayi ke tilasta musu ciki".
Amma Minji ta ce tana godiya tana da hukuma. "Muna rukunin farko da aka zaɓa. Kafin a ba mu, ya kamata mu samu yara. Amma daga baya muka zaɓi ba za mu yi ba saboda za mu iya."
'Da tuni ina da yara 10 da na so'
Idan muka koma gidan Yejin, bayan cin abincin rana da kawayenta suna duba littatafansu da kuma wasu sauran abubuwa.
Akwai gwale-gwale a rayuwar da ake yi a Korea, Yejin ta yanke shawarar ta koma New Zealand. Ta farka da wata safiya ta ga cewa babu wanda zai tilasta mata rayuwa a nan.
Ta yi bincike kan wacce ƙasa ce ta fi bai wa mata dama, kuma ta gano New Zealan ce ke kan gaba. " Ƙasa ce da ake biyan maza da mata albashi ba tare da banbanci ba," in ji ta, wani abu da hankali ba zai ɗauka ba.
Na tambayi Yejin da ƙawayenta, idan wani abu ya sauya musu ra'ayi kan hakan fa?
Minsung ta amsa cikin mamaki. "Ina son samun 'ya'ya. Ina son haihuwar 10 idan zan iya," To mai zai hana ki? na tambaye ta, 'yar shekara 27 ta shaida mini tana madigo a baya ma tana da abokiyar zama.
An haramta auren jinsi a Korea ta Kudu, Kuma an haramta matan da ba su da aure su yi amfani da maniyyi wasu domin su ɗauki ciki.
"Da fatan rana guda wannan lamarin zai sauya, ta yadda zan iya aure da wadda nake so kuma mu haihu," in ji ta.
Amma da alama 'yan siyasa na jan ƙafa wajen nisa da kuma haɗarin da wannan tarnaki ke da shi.
A wannan watan, Shugaban Korea ta Kudu Yoon Suk Yeol ya amince da cewa yunkurinsu da shawo kan wannan matsala "ya ci tura".
Ya ce wannan gwamnatin za ta magance matsalar ƙarancin haihuwa a matsayin "matsalar gwamnati" - amma har yanzu ana duba yadda za a mayar da hakan zuwa doka.
A farkon watan nan, na tuntubi Yejin da ke New Zealand, inda take zaune sama da watanni uku.
Tana ta farin ciki kan sabuwar rayuwarta da sabbin ƙawayenta, da kuma aikin da take a wata madafa. "Rayuwar aikina da sauran rayuwata sun daidaita," in ji ta. Ta kuma tsara yadda za ta haɗu da ƙawayenta a wannan makon.
"Ina ganin yadda ake girmama ni a wajen aiki kuma mutane ba sa yanke hukunci kanmu," in ji ta.
"Hakan ya sa ko son zuwa gida ba na yi."