Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Saliyo na 2023

Asalin hoton, Reuters
An bayyana Julius Maada Bio a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar Saliyo, amma 'yan adawa sun ce suna da ja a kan sakamakon.
Alƙaluman hukuma sun ce Mista Bio ya samu kashi 56% na ƙuri'un da aka kaɗa. Yayin da babban abokin takararsa, Samura Kamara yake biye masa.
Bayan fitar da rukunin farko na sakamakon a ranar Litinin, Dr Samura Kamara ya bayyana shi da cewa "fashi ne da rana ƙiri-ƙiri".
An yi zaɓen ne ranar Asabar cikin tsakiyar zaman ɗar-ɗar sai dai Shugaba Bio ya yi kira ga al'ummar Saliyo su "tabbatar sun zauna lafiya".
Dr Samura Kamara wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar All People's Congress (APC) ya yi zargin cewa ba a bar jami'an jam'iyyarsa sun tantance ƙuri'un da ake kaɗawa ba.
Masu sa ido na Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila sun nunar da matsalolin fayyace gaskiya wajen ƙidaya ƙuri'un.
Kwanaki ƙalilan kafin zaɓen, jam'iyyar APC ta yi ƙorafe-ƙorafe game da hukumar zaɓe ta Saliyo. Sai dai, hukumar ta dage a kan cewa ta ɓullo da matakan da za su tabbatar da adalci.
Zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa da na ƙananan hukumomi na zuwa ne bayan wani yaƙin neman zaɓe da ya yi dumu-dumu da tashe-tashen hankula.
A cikin makon jiya, sai da jam'iyyar APC ta yi zargin cewa 'yan sanda sun harbe wani mai goyon bayanta, ko da yake jami'an tsaron sun musanta.
Jam'iyyar ta ce an kuma kashe ɗaya daga cikin wani magoyin bayanta lokacin da dakarun tsaro suka yi ƙoƙarin tarwatsa cincirindon mutanen a wajen shalkwatar APCn da ke Freetown ranar Lahadi.
'Ya'yan jam'iyyar Maada Bio Sierra Leone People's Party (SLPP), sun ce abokan hamayya sun far musu a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe.
Wannan ne zaɓen Saliyo na uku tun bayan yaƙin basasar ƙasar wanda ya zo ƙarshe a shekara ta 2002.
A ranar Asabar, 24 ga watan Yuni ne aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Saliyo.
Manyan ƴan takara sun haɗa da shugaban ƙasa mai ci, Julius Maada Bio na jam'iyyar SLPP sai kuma ɗan takara mai hamayya, Samura Kamara na jam'iyyar APC.
Akwai yiwuwar wayarku ba za ta iya nuna wannan zanen ba







