Farashin burodi zai ninka nan gaba kaɗan, in ji masu gidajen burodi na Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban masu gidan burodi a Abuja, babban birnin Najeriya, Alhaji Ishak Aldul-Rahim ya ce yanzu haka tsadar man dizel ta sanya su cikin mawuyacin hali.
Ya ce "Shekaran jiya na sayi man dizel a kan Naira ɗari takwas da talatin kan kowace lita amma daga baya na koma an ce ya zama Naira dubu ɗaya da ɗari biyar kan kowace lita, ban san yadda za mu ƙare ba," in ji shi, a hirarsa da BBC.
Baya ga haka nan ya ce man na dizel yana ƙaranci a wuraren sayarwa.
A cewar sa baya ga tashin farashin mai, kusan farashin ɗaukacin abubuwan da suke buƙata wajen haɗa burodin sun tashi.
Alhaji Ishak Aldul-Rahim ya ce farashin wasu kayan da suke buƙata domin haɗa burodi ya ninka har sau uku.
Ya ƙara da cewa "Ina ganin da wuya ne farashin burodin da muke sayarwa 500 ba zai koma dubu ɗaya ba."
Dama dai tuni masu masana'antu suka koka game da hauhawar farashin man na dizel babu ƙaƙƙautawa a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin ƙarancin wutar lantarki.
Yanzu haka dai ƙungiyar dillalan man dizel ta ce idan hukumomi ba su ɗauki matakan da suka dace ba to kuwa farashin man zai zarce Naira dubu ɗaya daga farashinsa a hukumance, wato Naira ɗari shidda da hamsin da huɗu.
Mataimakin shugaban ƙungiyar masu masana'antu ta Najeriya Alhaji Ali Sufyanu Madugu ya ce a makon nan an sayi man na dizel a kan kudi Naira ɗari takwas da arba'in zuwa Naira ɗari takwas da hamsin a birnin Kano.
A cewarsa tashin farashin man ya shafi farashin kayan da kamfanoninsu ke samarwa.











