Matsalar tsaro: Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci a toshe layukan wayar mutanen da 'yan bindiga suka sace

Majalisar wakilan Najeriya

Asalin hoton, N Assembly

Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ƙamari a Najeriya musaman a yankin arewa maso yammaci da tsakiyar kasar, majalisar wakilan ƙasar ta buƙaci a soma toshe layukan wayoyin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Majalisar ta ce ta hanyar toshe layukan waɗanda aka sacen, 'yan fashin daji za su rasa hanyar cinikin kuɗin-fansa da dangin mutumin da suka sace.

'Yan fashin daji na ci gaba da cin karensu babu babbaka a haren-haren da suke kai wa kauyuka da garuruwa inda suke yin awon gaba da mutane domin garkuwa da su a basu kudin fansa.

Sai dai duk da cewa jami'an tsaron kasar na cewa ana daukar matakan dakile matsalar, kawo yanzu dai taƙi ci taƙi cinyewa

Honorabil Abdullahi Balarabe Salame, ɗan majalisar wakilai ne kuma yana cikin wadanda suka gabatar da wannan bukata a zauren Majalisar.

Ya ce; "Mutanen nan dai mun ga duk manufarsu ita ce kudi sannan don kudin da suke samu shi yasa suke kashe mutane, shi ya sa suke daukar mutane.

"Ya kamata mu samu wata hanya wadda za ta hanasu samun wannan kudi, idan sun dauki mutum ba za su sami kudi ba."

Ɗan majalisar ya ci gaba da cewa "ni na yi tunanin cewa mu ba ma'aikatar sadarwa umarni daga yanzu duk mutumin da aka dauke tare da wayarsa su toshe layin, saboda da wayoyin mutane ake cinikin kudin-fansa."

Honorabil Salame ya ce ya nemi majalisar ta umarci ministan sadarwa na kasar da su toshe duk wani layi wanda ya ke da alaka da laifi na daukar mutane ko na kashe-kashe ko na Boko Haram da sauransu kuma majalisa ta amince da wannan bukata ta sa.

Sai dai kuma ko matakin zai yi tasiri musamman idan aka dubi cewa 'yan uwa wadanda aka sace kan shiga mawuyacin hali da firgici sakamakon 'yan uwansu da ake garkuwa da su.

Wasu na ganin cewa wannan zai iya jefa rayuwar wanda aka sace cikin hadari.

Majalisar ta nuna damuwa a kan yadda ake ci gaba da samun karuwa a yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare haren 'yan fashin daji.

Hari na baya-baya nan wanda ake gani shi ne ya fi muni ya faru ne a jihohin Filato da Taraba da Binuwai inda mutum kusan 200 sun rasa rayukansu.