Kasuwar sayen ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Ancelotti, Ronald Koeman, Charly Musonda, Reece James

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta ce ba ta dabbacin ita ce za ta dauki dan kwallon Norway, Erling Braut Haaland, yayin da Real Madrid ke son rarrashin dan kwallon ya kara kaka daya a Borussia Dortmund daga nan sai ta dauke shi. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Tsohon dan wasan Real Madrid, Guti ya ce kungiyar Santiago Bernabeu ba za ta iya sayen Haaland ba, idan ta kasa daukarsa a karshen kakar bana. (El Chiringuito, via Goal)
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti na son daukar dan wasan Inter Milan, Nicolo Barella, idan hakan ta faru za a saka shakku kan makomar Toni Kroos, mai shekara 32 a Bernabeu. (El Nacional - in Spanish)
Kungiyoyi da daman a sha'awar sayen dan kwallon tawagar Faransa, Aurelien Tchouameni da suka hada da Chelsea da Liverpool da Paris St-Germain da Real Madrid, to sai dai Monaco ba za ta sallama shi kan kasa da fam miliyan 42 ba. (Foot Mercato - in French)
Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya ce bai da masaniya ko dan kwallon tawagar Argentina, PauloDybala zai ci gaba da taka leda a kungiyar a badi, bayan da yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar nan. (DAZN, via Football Italia)
Dan wasan Brazil, Marcal, zai bar Wolves, idan kwantiraginsa yak are a karshen kakar nan, zai koma taka leda a Botafogo a kasarsa. (Globo Esporte)
Tsohon wanda ya horar da Barcelona, Ronald Koeman na tattaunawa domin karbar aikin jan ragamar tawagar Netherlands, domin maye Louis van Gaal, wanda yarjejeniyarsa zai kare bayan kammala gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022. (NOS - in Dutch)
Roma da Hellas Verona na son rige-rigen daukar dan kwallon Chelsea, Charly Musonda,wanda ke shirin barin Stamford Bridge da zarar an kammala kakar bana. (Goal)
Manchester United na bibiyar mai tsaron raga, Benjamin Siegrist, wanda ke wasa a Dundee United, wanda yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar tamaula ta bana. (Mirror)
Dan wasan Chelsea, Reece James zai bar tawagar kwallon kafa ta Ingila, inda ake sa ran mai taka leda a Crystal Palace, Tyrick Mitchell zai maye gurbinsa. (Mail)











