Super Tucano: Abin da ya sa Najeriya ba ta fara amfani da sabbin jiragen yakin da ta saya a Amurka ba

Asalin hoton, NASS
Bayanai na ta ic gaba da bayyana kan dalilan da suka sa har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta fara amfani da sabbin jiragen yaƙin da ta saya daga Amurka ba wato Super Tucano.
Tun bayan isowar jiragen Najeriya a watan Yuli bayan kammala ciniki, ƴan ƙasar da dama sun saka ran cewa nan da nan za a fara amfani da su wajen kai wa ƴan fashin daji hare-hare don murƙushe su, musamman a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Sai dai rahotanni sun ce akwai wani babban lamari da ke jawo tsaiko wajen aiwatar da hakan, wanda bai wuce sharaɗin da ke dabaibaye da sayen jiragen ba tun farko, wanda Amurka ta sanya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta shaida wa Majalisar Dokokin ƙasar cewa, tun farko Amurka ta yarda ta sayar da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano 12 ne idan za a yi amfani da su a kan ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya ne kawai, ban da ƴan fashin daji.
Kenan batun a yi amfani da jiragen wajen yaƙi da ƴan fashin dajin da ke addabar yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya bai taso ba, tun da har yanzu gwamnatin Najeriya da gwamnatocin ƙasashen waje ba su ayyana su a matsayin ƴan ta'adda ba.
Ana ta ƙara samun kiraye-kirayen a ɗauki wannan mataki, don babu dama ga dakarun tsaron ƙasar su kai ƙarin kayan yaƙi da nufin murƙushe 'yan fashin daji da suka addabi yankunan arewa maso yamma da sassan arewa ta tsakiya.
Amma Majalisar Wakilan Najeriyar ta bayyana fatan cewa nan ba da daɗewa ba, Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu kan ƙudurin da ke neman ayyana 'yan fashin daji a matsayin 'yan ta'adda.

Buƙatar ayyana ƴan fashi a matsayin ƴan ta'adda

Shugaban kwamitin kula da harkokin sojin ƙasa a majalisar wakilan Najeriya Honourable Abdurrazaƙ Namdaz, ya ce dukkanin majalisu wakilai da na dattawa sun amince shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda, har ma sun yi ƙuduri sun aika masa, kuma suna kyautata zaton cewa zai amince da wannan bukata''
A cewarsa "Abubuwan da suke aikatawa sun ma fi na ƴan ta'adda, kana ganin kwanan nan an kashe mutane sun fi 50 a Sokoto, ba za a bar mutanen da suke kashe mutane haka kawai su ci gaba da cin karensu ba babbaka."
Ya ƙara da cewa "Kashe-kashe na yawa a ƙasar nan, ana kashe mutane yara da mata, amma sai a yi ta tafiya a kan maganar cewa akwai yancin kare ɗan adam, mun yarda akwai wannan, amma ba zai yi wu a zuba musu ido haka kawai ba."
Masana harkokin tsaro dai sun yi imanin cewa ayyana yan fashin dajin a matsayin ƴan ta'adda zai ba da damar zagewa a yi yaƙi da ƴan fashin dajin da suke ci gaba da tsananta hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Masanan na da ra'ayin cewa ayyana ƴan bindigar a matsayin ƴan ta'adda, zai sa gwamnatin Najeriya ta samu tallafi daga ƙasashen duniya, da kuma ware su daga cikin jama'a don yaƙi da su ka'in da na'in.

El-Rufa'i ma ya koka
Shi ma gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda ake fama da matsalar ƴan fashin sosai, ya nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana 'yan bindigar a matsayin 'yan ta'adda "saboda sojoji su samu damar kashe su ba tare da wata matsala ba", in ji shi.
"Mu a Kaduna mun sha neman a ayyana 'yan fashin nan a matsayin 'yan ta'adda. Mun rubuta wasiƙu ga gwamnatin tarayya tun 2017 muna neman a yi hakan saboda ayyana su ne kaɗai zai bai wa sojoji damar karkashe waɗannan 'yan fashin ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga ƙasashen duniya."

Asalin hoton, Kadun Govt
Sabon rahoton da aka gabatar wa El-Rufai a ranar Laraba, ya nuna cewa mutum 343 aka kashe a Kaduna daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021 sakamakon ayyukan 'yan fashi da kuma rikicin ƙabilanci a jihar.
Haka nan, 'yan fashin dajin sun sace mutum 830 cikin wata ukun da rahoton ya bayar da bayanai a kai tare da raunata 210.
Sannan ya shawarci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matasa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma aikin bayar da tsaro don yaƙar 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane.
Da yake magana jim kaɗan bayan miƙa masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar, El-Rufai ya ce babu wata hanyar yaƙi da 'yan fashin daji illa "yi musu ruwan wuta a lokaci guda", abin da ya sa yake son a ɗauki matasa 774,000 aikin.
"Ina kira ga jihohi 36 da su ɓullo da wani shirin gaggawa na ɗaukar mutane aiki a rundunonin tsaro. Gwamnati ka iya sauya halin da ake ciki idan ta ɗauki matasa 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma a faɗin ƙasa.
"Hakan zai zama gagarumin adadi na dakaru a fagen daga tun bayan yaƙin basasa. Adadin sabbin dakaru 774,000 a filin yaƙi zai kasance babbar hanyar gamawa da miyagu da kuma samar da aikin yi."











