Sulhu kan rikicin Fulani: Ko tsarin da aka bi kan a kudu maso yammacin Najeriya zai yi aiki a Arewa?

Wasu 'yan Najeriya na ci gaba da yabawa da yadda aka daidaita rikicin Fulani makiyaya bayan da gwamnonin jihohin kudu-maso-yammacin kasar suka hada gwiwa da wasu takwarorinsu na Arewa, da kuma ƙungiyoyin Fulani domin magance matsalar tsaro a yankin.
A ƴan kwanakin nan ne gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da wasu matasa a jihar Oyo suka umarci Fulanin da su fice daga dazukan jihohinsu, bisa zargin suna bai wa miyagu mafaka. Amma makiyayan sun musanta zargin.
Wannan ya janyo zazzafar muhawara a faɗin ƙasar duk da cewa daga baya an cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu bayan tattaunawar da aka kwashe wuni guda ana yi a Akure, baban birnin jihar Ondo.
Cikin abubuwan da aka cimma matsaya har da hana kiwon dare da haramta wa kananan yara yin kiwo da yi wa makiyaya rijista da sauransu.
Sai dai wasu masana na ganin cewa akwai bukatar gwamnonin arewacin kasar su yi irin wannan yunkurin, tunda matsalar tabarbarewar tsaron ta fi muni a yankin.
Masana harkokin tsaro da dama sun yaba da matakin da gwamnonin yankin Yarabawa suka dauka cikin gaggawa.
Sannan an tashi taron neman mafitar duka ɓangarorin biyu na farin ciki da matsayar da aka cimma.
Fulanin sun amince za su hada kai da mahukunta wajen ankarar da su, tare da taimakawa wajen kama miyagu idan sun rabe su.
Wasu gwamnoni daga arewacin Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan jituwar.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ya sa masana harkokin tsaro ke cewa akwai bukatar gwamnonin arewa su yi koyi da takwarorinsu na kudu, ganin cewa matsalar satar mutane da ake zargin wasu bata-gari a tsakanin Fulani na yi ta fi muni a arewacin kasar.
Barrsita Bulama Bukarti, jami`i ne da ke gudanar da bincike a kan harkar tsaro a nahiyar Afirka a Cibiyar Tony Blair kuma ya ce ana iya haɗa kai da kungiyoyin Fulani wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa.
"Lokacin da aka sace ɗalibai a garin Kanƙara a jihar Katsina, shugaban ƙungiyar Miyetti Allah aka ce an ɗauko an shiga daji da shi har aka samu karɓo waɗannan yara.
"Wannan ya nuna cewa ƙungiyar ta Miyetti Allah na da ƙarfin faɗa a ji a tsakanin masu aikata irin wannan laifi," a cewar Bulama Bukarti.
Ya ce da alama masu aikata irin waɗanann miyagun halaye na ganin mutuncin ƙungiyar Miyetti Allah.
Sai dai ba ƙungiyoyin Fulanin sun ce duk da yake suna son shiga irin wannan tsari amma suna fuskantar kalubale daga yankin Arewa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta ƙasa Alhaji Muhammadu Kiriwa ya ce ya san cewa ƙungiyarsa a shirye take ta ba da gudunmuwa don samar da zaman lafiya a ko ina a Najeriya a matsayinsu na `yan arewa.
"Babu inda ba mu kai ƙoƙon bararmu ba kan wannan lamari. Ai mun je Katsina, mun je Zamfara kuma duka an yi nasara," a cewarsa.

Asalin hoton, Google
Sai dai ya ce hukumomin yankin ba su dauki batun da muhimmanci ba shi ya sa har yanzu ake ganin kamar ba a samu ci gaba ba a ɓangaren harkar tsaro a waɗannan jihohin.
Baya ga kungiyar Miyetti Allah akwai ta Miyetti Allah Kautal Hore wadda ita ma tana daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke kare muradai da raya al`adu da walwalar Fulani a Najeriya.
Shugabanta Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, ya ce tun tuni matsalar ke damunsu yadda ake kuɗin goro wajen zargin Fulani da miyagun halaye, duk kuwa da cewa Uba kan haifi ɗa amma ba lallai ba ne ya haifi halinsa.
Ya ce a nasu bangaren har sun fara daukar matakan magance matsalar.
"Muna tare da Fulanin nan muna sane da dazuzzukan da suke, amma wani abun idan ba a neme ka ba sai ka ja baya," a cewarsa.
"Kwanakin baya na yi yunƙurin assasa ƴan banga na Fulani amma abin ya yi yawa, amma ban fasa ba," a cewarsa.
Ya ce yana goyon bayan duk wani abu da za a yi don ganin Fulani sun zauna lafiya.
Yanzu dai ido ya koma kan shugabannin arewa, musamman ma gwamnoni wajen ganin ko da wani darasin da za su koya daga takawarorin nasu na kudancin kasar wajen magance wannan matsala ta tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.











