Hotunan yadda ake wahalar man fetur a Birtaniya

Masu ababen hawa a Burtaniya na ci gaba da shafe tsawon sa'o'i a kan layukan sayen man fetur

Asalin hoton, SOPA Images

Bayanan hoto, Kusan makonni biyu kenan ana samun dogayen layuka a gidajen mai a Burtaniya. Kuma rahotanni sun nuna cewa gidajen mai 5,500 daga cikin 8,000 ba su da man kwata-kwata.
Duk da matakin hukumomi na tura rukunin wasu tankoki na ko-ta-b'aci don kai man fetur da yammacin jiya Laraba.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Duk da matakin hukumomi na tura rukunin wasu tankoki na ko-ta-b'aci don kai man fetur da yammacin jiya Laraba har yanzu lamarin bai inganta ba
Sakataren harkokin kasuwanci Kwasi Kwarteng ya ce fararen hula ne ke tuk'a tankokin man daga defo-defonsu a Cambridgeshire da West Yorkshire.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Sakataren harkokin kasuwanci Kwasi Kwarteng ya ce fararen hula ne ke tuk'a tankokin man daga defo-defonsu a Cambridgeshire da West Yorkshire...
Ya kuma ce sojoji za su fara aikin safarar man a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Ya kuma ce sojoji za su fara aikin safarar man a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
Firanminista Boris Johnson ya ce gwamnatinsa za ta ba da biza ga dirabobin tankokin mai 5,000 daga kasashen waje don su yi aikin dakon mai a kasar.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Firanminista Boris Johnson ya ce gwamnatinsa za ta ba da biza ga dirabobin tankokin mai 5,000 daga kasashen waje don su yi aikin dakon mai a kasar.