Jihar Plateau: Ƙungiyoyin arewa na neman a hukunta waɗanda suka kashe Musulmai a jihar

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyin farar-hula na ci gaba da yin Allah-wadai da kisan-gillar da aka yi wa wasu matafiya Musulmi a jihar Filaton Najeriya a ranar Asabar din da ta wuce.

Kazalika kungiyoyin sun yi zargin cewa rashin zartar da hukunci ne ke sa ya wasu mutane yin irin wannan aika-aikar.

Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin `yan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.

Kungiyoyin farar-hular, sun nuna takaici da kuma alhini game da kisan-gillar da aka yi wa matafiya Musulmin a gada-biyu da ke titin Rukuba a cikin birnin Jos...kisan da hatta mahukunta na zargin `yan kabilar Irigwe da aikatawa, duk kuwa da cewa shugabanninsu sun fito sun musanta.

Lalong

Asalin hoton, LALONG

Sai dai ganin cewa ba wannan ne karon farko da ake tsare matafiya ana halaka su a wasu sassan jihar Filaton ba, kungiyoyin sun bayyana cewa da wuya masu irin wannan aika-aikar su daina, tun babu wani hukuncin da ake musu a zahiri.

Kungiyar matasan arewa-maso-gabashin kasar, wato Movement Of Northeast Youths Organisation Forum ta ce al`ummarta na cikin majibinta hanyoyin da suka ratsa jihar Filato, kuma a lokuta da dama kan mutanensu irin wannan tsautsayi ke fadawa a duk lokacin da irin wannan rikici na tsare matafiya ya barke.

Shugaban ƙungiyar Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham, ya bayyana wa BBC cewa ba za su lamunci irin wannan ba, don haka dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa an tsaya tsayin daka wajen hukunta masu hannu a wannan kisa da aka yi.

A cewarsa: "Dole ne gwamnati ta kama shugabannin yankunan da ake irin wadannan kashe-kashe, domin ba yadda za ta yiwu a ce mutane 50 ko 60 su tare hanya amma sarakunansu ba su sani ba."

Kwacam

Asalin hoton, YOUTUBE

"Muna son gwamnonin su su gaya musu cewa suna fa da mutane a yankunan da muke, wallahi ba za mu yarda ba,, idan kuma suna ganin za su sake yin hakan su ƙara su gani", in ji shi.

Ita ma gamayyar kungiyoyin farar-hula da ke arewacin Najeriya, ta yi misali da kisan-gillar da aka yi wa wani babban jami`in Sojin kasar a jihar Filaton, mai suna Janar Idris Alkali mai ritaya, wanda tun ana kidayar watanni da kama wadanda ake zargi da kisansa har an koma kidayar shekaru, amma shiru kake ji, babu wani hukunci da ya biyo baya.

Shugaban kungiyar amintattun kungiyar Nastura Ashiru Sharif, ya shaida wa BBC cewa sun yanke kauna game da ikirarin da mahukunta ke yi cewa za a hukunta mutanen da ake zargi da kashe matafiyan.