Jihar Zamfara : Mutanen wasu ƙauyuka a Shinkafi sun tsere daga gidajensu

Asalin hoton, AFP
Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton yaran kasurgumin shugaban 'yan bindigan nan na jihar Zamfara da ake kira Turji ne, sun far wa mutanen wasu kauyuka 24 da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Rahotannin da BBC ta tattara sun nuna cewa dama ya ba wa mutanen ƙauyukan wa'adin awa hudu su fice daga gidajensu ko kuma ya far musu.
Mutanen garuruwan sun ce ya fusata ne saboda jami'an tsaro sun kama masa mahaifinsa a jihar Jigawa, a don haka ne ya lashi takobin huce haushinsa a kan jama'a matsawar ba a saki mahaifin nasa kafin babbar salla ba
Bayanai dai sun ce maharan sun auka wa mutane ne tun ranar Juma'ar da ta gabata, suna fasa shaguna suna kwashe kayan abinci, tare da kama wasu mutanen da kuma hallaka wasu.
Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa yawan mutanen da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su kawo yanzu haka ya kai kusan 150.

Ƙauyukan da aka kai wa harin sun hada da Kurya, da Keta, da Kware, da Badarawa, da Marisuwa, da Maberaya da kuma ƙarin wasu da dama.
Bayan kai hare-hare a kauyukan, yan bindigan sun kuma sace matafiya da dama a kan hanyar Gusau zuwa Sokoto.
Mutanen garin sun bayyana cewa dama Turji, wato jagoran 'yan bindigar ya ce yadda mahaifinsa zai yi babbar salla a wajen hukuma haka suma mutanen da zai kama za su yi sallar a wajensa, sannan kuma zai kashe wasu.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa "An kira shi a wayar tarho yayin wani taro tsakanin mutanen gari da jami'an tsaro amma bai zo ba saboda kama mahaifinsa, yana mai cewa shi ne yake kai hare-hare, an kuma san inda ya ke, saboda haka babu wani dalili da zai sa a kama mahaifinsa da bai ji ba bai gani ba''.











