Ahmad G. Ahmad: 'Yan bindiga sun harbe dan majalisar dokokin jihar Zamfara

Asalin hoton, Shi'isu Shinkafi
Wasu mutane da ake zargi 'yan bindiga ne sun harbe wani dan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wasu makusantan dan majalisar dokokin sun shaida wa BBC cewa an harbe Alhaji Ahmad G. Ahmad ne a jihar Katsina yayin da yake kan hanyar zuwa birnin Kano.
Shi ne yake wakiltar karamar hukumar Shinkafi a majalisar dokokin jihar ta Zamfara.
An yi jana'izarsa a masallacin Malam Umar Kanoma da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara da ranar Laraba.
Gwamnatin jihar Zamfara ta fitar da sanarwar ta'aziyyar marigayin mai wakiltar karamar hukumar Shinkafi, wanda ko a jiya Talata ma yana wurin taron sauya shekar gwamnan jihar daga jamiyyar PDP zuwa APC.
Sanarwar ta ambato gwamnan yana cewa: "Ko a jiya muna tare da Honorabul Muhammad wajen shirye-shiryen ficewa ta daga PDP zuwa APC, kuma ya bayar da gudunmowarsa sosai a wajen taron, ba mu san cewa yana gudanar da aikinsa na ƙarshe ba ne a duniya."
Sannan gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya ji kan mamacin tare da kai rahama ƙabarinsa.
Wani makusancin Alhaji Ahmad G. Ahmad da ba ya so a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Talata a jihar Katsina yayin da dan majalisar da dansa da kuma wani amininsa suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Kano.
"Suna kan hanyar zuwa Kano domin kai dansa filin jirgi inda zai tafi makaranta a Sudan, sai 'yan bindiga suka yi musu kwanton-bauna a kusa da kauyen 'yan Kara da ke hanyar Funtua.
"Sun kashe dan majalisar shi kadai, amma sauran mutanen sun tsira. Hasalima, dansa ne ya rike sitiyarin motar shi ya sa ba ta hantsila ba," in ji majiyarmu.

Asalin hoton, Sha'isu Shinkafi











