Bazoum Mohamed: Zababben shugaban Jamhuriyar Nijar ya jinjina wa 'yan kasar

Asalin hoton, EPA
A Jamhuriyar Nijar, hankula sun karkata wajen Kotun Tsarin Mulkin ƙasar, wadda za ta fitar da matsaya a kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.
Da maraicen jiya ne, Hukumar zaɓe ta CENI ta sanar da sakamakon wucin gadi da ya bayyana d'an takarar PNDS Tarayya, Bazoum Mohammed a matsayin wanda ya lashe da kuri'u fiye da miliyan biyu da rabi.
'Yan adawa dai sun yi watsi da sakamakon, har ma an samu zanga-zangar wasu matasa a unguwannin birnin Yamai.
Yayin da ya ke yin jawabi ga magoya bayan nasa a shakwatar hukumar zaben da ke Niamey, Bazoum ya gode mu su saboda abin da ya kira jajircewar da su ka yi har jam'iyyarsa ta sami nasara:
"Da farin ciki mai dumbin yawa na ke la'akari da wadannan abubuwan. Kuma da kankan da kai na ke jinjina wa jama'ar Nijar."
Mahaman Kassoum Moktar shi ne shugaban jam'iyar CPR Inganci kuma mamba cikin ƙawancen jam'iyu 21 da ya marawa Bazoum Muhammed baya kuma a tattaunawarsu da wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou, ya nuna jin dadinsa kan wannan nasara ta dan takararsu.
"Ga dukkan 'yan Nijar gaba daya, wadanda su ka zabi Bazoum, da ma wadanda ba su zabe shi ba, Allah ya saka mu su da alheri. Wannan ita ce babban sakon da mu ke son mika wa a daidai wannan lokaci da hukumar zabe mai zaman kan ta CENI ta tabbatar cewa shi ne zababben shugaban Nijar."
Abokin hamayyarsa kuwa, wanda shi ne tsohon shugaban kasar Mahamane Ousmane, shi da magoya bayansa sun yi watsi da sakamakon zaben, inda magoya bayan nasa su ka fita titunan Niamey, wanda shi ne babban birnin kasar su na zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaben kuma su na kona tayoyi.











