Ana dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Guinea

A kasar Guinea da ke yankin Afirka ta Yamma, masu zabe sun yi dogayen layuka duk tsawon yinin ranar Lahadi a rumfunan zabe duk da ruwan saman da aka sharara.
Kusan mutum miliyan 5.5 ne suka cancanci yin zaben, sai dai za a shafe kwanaki kafin a fitar da sakamakon zaben.
Bambance bambancen kabilanci da na siyasa sun sa ana fargabar barkewar rikici yayin da Shugaba Alpha Conde mai shekara 82 ke neman wa'adi na uku.
A kalla mutum fiye da hamsin suka rasa rayukansu cikin watannin da aka shafe ana zanga-zangar adawa da shirin tsawaita mulkin shugaban kasar
Babbar matsalar da ke ci wa 'yan kasar Guinea masu adawa da mulkin Shugaba Alpha Conde ita ce sauya tsarin mulkin kasar da yayi domin sake tsayawa takara a karo na uku.
Sabon tsarin mulkin da masu zabe suka aminta da samarwa a watan Maris zai iya ba Shugaba Conde karin shekara 12 a karagar mulkin kasar.
A babban zaben da ya gudana, Mista Conde na fafatawa ne da wasu tankara 11, sai dai wasu jam'iyyun siyasa sun kauarcewa zaben.

Asalin hoton, AFP
Yayin da yake kada kuri'arsa Shugaba Conde ya bukaci a yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana:
"Fata ta ita ce a yi zabe cikin walwala, bisa tsarin dimokradiyya kuma wanda babu kumbiya kumbiya. Za mu tabbatar da akwai tsaro a rumfunan zabe."
Ya kara da cewa, "Saboda haka muke kira ga dukkan 'yan takara da su guji ayyukan da za su tayar da husuma, kuma za mu sanar da hukumomin cikin gida da na kasa da kasa idan muka sami wasu da ke osn tayar da zaune tsaye."

Asalin hoton, AFP
Sai dai babban abokin hamayyar shugaban kasar na siyasa, Cellou Dalein Diallo ya gargadi hukumar zaben kasar da kada ta bari a yi magudi, kuma ya bayyana karfin gwuiwa cewa shi ne zai lashe zaben:
"Ina kira ga dukkan magoya baya na da su nuna juriya da halin ya kamata domin a sami yin wannan zaben cikin tsari mafi tsafta."
Ya kara da cewa ba shi da shakku kan sakamakon wannan zaben, "shi ne ya sa ba na son tashin hankali, wanda ka iya kawo cikas ga nasarar da nake kan hanyar samu."
Shugaba Conde ne zababben shugaba na farko karkashin tafarkin demokradiyya, amma ya karkata zuwa gefen masu mulkin kama karya.
Guinea na fuskantar matsananciyar matsalar tattalin arziki, inda dumbin albarkatun da ke jibge a karkashin kasa ba su kai ga talakawan kasar ba, matakin da ya haifar da talauci da rashin aikin yi.











