Matsalar Tsaro: 'Yan bindiga sun sace ɗalibai da malamarsu a wata makaranta a Kaduna

..

Asalin hoton, AFP

'Yan bindiga sun kai hari a wata makaranta da ke wani kauye a jihar Kaduna da ke Najeriya inda suka sace dalibai da dama tare da malamarsu.

Wani mazaunin kauyen Damba-Kasaya a karamar hukumar Chukun ya shaida wa BBC Hausa cewa 'yan bindiga a kan babura sun kai hari makarantar Prince Academy a ranar Litinin da safe inda suka tafka ta'asa.

A cewarsa, kawo yanzu akwai dalibai biyar da wata malamar makaranta da har yanzu suke hannun 'yan bindigar.

"Suna rike da dalibai biyar da malama daya wadanda bamu san inda suka kai su ba," in ji ganau din.

"Lokacin da suka shigo cikin kauyen sun yita harbi a sama kafin su shiga cikin makarantar kuma suka sace daliban da ke shirin rubuta jarabawar aji uku".

Bayanai sun ce wani manomi da ake sace a gonarsa ya kubuta daga hannun 'yan bindigar.

Rundunar 'yan sanda jihar Kaduna ta ce tana gunadar da bincike kan lamarin kafin ta fitar da sanarwa.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun kuma sun kai hari a cikin wata majami'a a kauyen tare da kona kayayyakin kida na cocin.

Mazaunin garin ya kara da cewa jami'an tsaro na sojoji sun isa kauyen jim kadan bayan kaddamar da harin, amma basu kai ga ceto daliban ba.

An kashe mutum 1,126 cikin wata shida a arewacin Najeriya

Wannan layi ne
Zamfara na cikin jihohin da wannan bala'i ya fi addaba.

Asalin hoton, Zamfara government

Bayanan hoto, Kaduna na cikin jihohin da wannan bala'i ya fi addaba.

Kungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty Intanertional ta ce ƴan bindiga masu fashin daji sun kashe kimanin mutum 1,126 a jihohin arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.

A rahoton da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta ce ɗaruruwan mutane ne aka raba da gidajensu a jihohin Kaduna da Neja da Katsina da Filato da Taraba da kuma Zamfara inda aka ƙone gidaje aka kuma sace mutane.

Amnesty ta ce tun 2016 take bibiyar matsalar ƴan bindiga masu fashin daji da kuma rikicin makiyaya da manoma.

Ƙungiyar ta ce hukumomin Najeriya sun bar mutanen karkara a hannun ƴan bindiga da suka kashe ɗaruruwan mutane, wanda kuma ke ƙara haifar da tsoro da fargaba kan wadatuwar abinci a yankunan karkara.

Hukumomin Najeriya da suka musanta rahoton Amnesty, zuwa yanzu ba su fitar da wani martani ba game da rahoton ƙungiyar.

Wannan layi ne