Mesut Ozil ya ce yana nan daram a Arsenal har zuwa karshen 2021

Mesut Ozil sitting in the stand while a substitute for Arsenal

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Mesut Ozil bai murza leda a Arsenal ba tun a watan Maris

Ɗan kwallon Arsenal, Mesut Ozil ya ce zai ci gaba da murza leda a kulob din har zuwa karshen kwangilarsa a watan Yunin 2021.

Tsohon dan wasan Jamus mai shekaru 31, bai buga wasan gasar Premier ba tun a watan Yuni, kuma manajansa Mikel Arteta ya bayyana hakan "a matsayin hujjoji ne na kwallo"

Ozil ya musanta rahotannin da ke cewa kulob din na kokarin sallamarsa domin biyansa sauran kudin kwangilar da ta rage a kan fan dubu 350 a kowane mako.

"Abubuwan babu dadi amma ina son Arsenal," ya shaida wa mujallar the Athletic.

"Ni zan yanke shawarar lokacin da zan tafi ba jama'a ba," in ji Ozil.

Ozil ya koma Arsenal ne a kan fiye da fan miliyan 42 daga Real Madrid a 2013, amma sai ya fuskanci tsamin dangantaka tsakaninsa da tsohon manajansa Unai Emery.

Lokacin da aka nada Arteta a watan Disamban 2019, Ozil ya buga wasanni 10 jere kafin a tafi hutu saboda annobar korona.

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ozil ya nuna bacin ransa lokacin da aka sauya shi a wasansu da Man City

Amma tun da aka dawo murza leda an buga wasanni 13 kuma babu wanda ya bugawa Arsenal.