Geoffrey Onyeama: Buhari ya yi wa ministan da ya kamu da coronavirus addu'a

..

Asalin hoton, TWITTER/@NGRPRESIDENT

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa Ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama addu'ar samun sauƙi, bayan ya kamu da cutar korona.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, shugaban ya bayyana Mista Geoffrey a matsayin wani babban ginshiƙi a mulkinsa, kuma ya yaba masa kan irin ƙoƙarin da yake yi wurin daƙile yaɗuwar korona.

Mista Onyeama dai na ɗaya daga cikin 'yan kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa domin yaƙar cutar korona.

A ranar Lahadi ne dai ministan ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na huɗu.

A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Ministan ya zama shi ne farko da ya kamu da cutar korona a jerin ministocin Najeriya.

A watan Afrilun wannan shekara ne cutar ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, wanda kafin rasuwarsa shi ne babban hadimin shugaban Najeriya kuma aboki na ƙut da ƙut ga Geoffrey Onyeama.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Akwai da dama daga cikin 'yan siyasa a Najeriya da cutar ta kama suka warke wasu kuma suka mutu.

Cikin waɗanda suka warke sun haɗa da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da na Bauchi Bala Muhammad da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.

Waɗanda cutar ta yi ajalinsu kuwa sun haɗa da Tsohon Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi da Tsohon Darakta a kamfanin NNPC Engr Sulaiman Achimugu da kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC reshen Arewa maso Yamma, Inuwa Abdulkadir.

Sama da mutum 36,000 cutar korona ta kama a Najeriya, kusan mutum 15,000 suka warke inda kuma kusan mutum 800 suka mutu, kamar yadda hukumar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa taƙasar NCDC ta bayyana.