Abubuwa huɗu kan dokar hana cin zarafin ɗalibai a Najeriya

OVIE OMO-AGEGE/FACEBOOK

Asalin hoton, OVIE OMO-AGEGE/FACEBOOK

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Ovie Omo-Agege ne ya gabatar da kudurin dokar mai take ''Wani shirin doka wanda zai hana da ba da kariya da kuma hukunta masu fasikanci da dalibai a manyan makarantu

A ranar Talata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani kudurin doka da zai ba da kariya ga dalibai a manyan makarantun kasar, bayan yi masa karatu na uku.

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Ovie Omo-Agege ne ya gabatar da kudurin dokar mai take ''Wani shirin doka wanda zai hana da ba da kariya da kuma hukunta masu fasikanci da dalibai a manyan makarantu, da kuma wasu harkokin masu alaka da shi na shekara ta 2019.

An dai amince da kudurin dokar ne bayan duba da nazarin da majalisar dattawan ta yi a kan rahoton kwamitin da ke kula da abubuwan da suka shafi shari'a da take hakkin bil adama wanda ke da alhakin yin garanbawul akan dokar tare da kuma shirya yadda za a saurari bahasin jama'a a kan dokar.

An sake gabatar da kudurin a gaban majalisar dattawan tun a watan Oktoban da ya wuce inda kuma har aka yi masa karatu na biyu a watan Nuwamba.

Kudurin dokar ya kunshi abubuwa da dama da suka hada da hukuncin shekara 14 koma fiye da haka ga duk wanda aka samu ya ci zarafin daliba, akalla dai mutum zai iya shekara biyar a gidan yari ba tare da beli ba.

Daga cikin tanade-tanaden da ke kudurin akwai batun cewa:

  • Duk malamin da ya yi tarayya da daliba ko kuma ya bukaci yin tarayya da ita akwai hukunci akansa na shekara 14 ko kuma mafi kankantar hukuncin yin hakan shi ne shekara biyar ba tare da tara ko beli ba.
  • Haka duk wanda ya tursasawa daliba yin lalata da wani ma irin wannan hukunci zai fuskanta, sannan duk malamin da aka samu ya runguma ko sumbata ko taba wani bangare na jikin daliba ma akwai hukunci akansa.
  • Sannan duk malamin da aka samu ya aika da wani sako na batsa ko ta hannu ko kuma ta wata kafar sadarwa ga daliba akwai hukunci akansa.
  • Haka duk malamin da yi zancen batsa da kifta idanu da nufin wani batanci ga daliba akwai hukunci akansa.

An dai sake gabatar da wannan kudurin ga majalisar dattawan ne kwana biyu bayan BBC ta yi wani rahoton na musamman inda aka bankado asirin wasu malaman jami'a biyu a jami'ar Legas da kuma wani malamin jami'a a Ghana da suke cin zarafin dalibansu mata domin neman makin jarrabawa.

Wannan rahoton na BBC ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu 'yan Najeriyar suka bayyana wannan halayya a matsyain rashin tarbiyya a jami'oin kasar.

A yayin sauraron bahasin jama'a akan kudurin dokar, malaman jami'oi da ma'aikatan jami'o'i da kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwa tare da bukatar a yi gyara akan kudurin dokar don kawo karshen cin zarafin dalibai a makarantu.