Geoffrey Onyeama: Coronavirus ta kama ministan Buhari

Lokacin karatu: Minti 1

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya kamu da cutar korona.

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na huɗu.

A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.

Ministan ya zama shi ne farko da ya kamu da cutar korona a jerin ministocin Najeriya.

A watan Afrilun wannan shekara ne cutar ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, wanda kafin rasuwarsa shi ne babban hadimin shugaban Najeriya kuma aboki na ƙut da ƙut ga Geoffrey Onyeama.

Akwai da dama daga cikin 'yan siyasa a Najeriya da cutar ta kama suka warke wasu kuma suka mutu.

Cikin waɗanda suka warke sun haɗa da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da na Bauchi Bala Muhammad da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.

Waɗanda cutar ta yi ajalinsu kuwa sun haɗa da Tsohon Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi da Tsohon Darakta a kamfanin NNPC Engr Sulaiman Achimugu da kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC reshen Arewa maso Yamma, Inuwa Abdulkadir.

Sama da mutum 36,000 cutar korona ta kama a Najeriya, kusan mutum 15,000 suka warke inda kuma kusan mutum 800 suka mutu, kamar yadda hukumar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa taƙasar NCDC ta bayyana.