Joe Biden ne dan takarar jam'iyyar Democrat a zaben 2020

Mista Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Joe BIden, dan takarar mukamin shugaban Amurka

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya sami yawan wakilan da yake bukata a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwani na jam'iyyar Democrat.

Wannan na nufin shi ne dan takarar jam'iyyar ta Democrat a hukumance, bayan da ya sami kuri'u 1,991 na dukkan wakilan da suka kada kuri'u.

Kididdigar ta tabbatar da abin da aka dade da sani game da nasarar ta Mista Biden tun tsakiyar watan Maris, lokacin da ya sha gaban abokin takararsa Sanata bernie Sanders, matakin da ya sa shi Mista Sanders din janyewa daga takarar a farkon watan Afrilu.

Mista Biden ya shafe gomman shekaru yana rike da mukamin sanata mai wakiltar jihar Delaware kafin daga baya ya zama mataimakin shugaban Amurka a 2009.

Wannan nasarar na nufin shi ne zai kalubalanci shugaba mai ci Donald Trump a zaben shugaban Amurka da zai gudana a watan Nuwamba mai zuwa.

Mista Biden ya lashe duka jihohi bakwai da suka gudanar da zzabukan fid da gwamni ranar Talata - su ne Maryland Indiana, Rhode Island da New Mexico, da Montana, da South Dakota da Pennsylvania da kuma Gundumar Columbia.

Da ma yana daf da samun kuri'un tun da aka fara hada alkaluman wadanda suka kada kuri'un.

A wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan ya cimma kuri'u 1,991, Mista Biden ya ce Amurka na bukatar jagoranci musamman a wanna lokaci.

A cikin sanarwar ya ce "Wannan mawuyacin lokaci ne a tarihin Amurka. Sannan siyasar Donald Trump ta raba kawunan Amurkawa ba zai haifar da da mai ido ba. Kasar nan na bukatar jagora. Jagoran da zai hada kanmu".

Babban Kwamitin Kasa na Jam'iyyar Democrat zai gudanar da babban taro na fid da gwani a tsakiyar watan Agusta inda jam'iyyar za ta tsayar da Mista Biden a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba.