Joe Biden ya lashe zaben South Carolina

Asalin hoton, Getty Images
Alkaluma daga wadanda suka kada kuri'arsu a zaben fitar da gwani na 'yan jam'iyyar Democrat na Amurka na cewa Joe Biden ne ya lashe zaben.
A wannan karon ana gudanar da zaben ne a jihar South Carolina, kuma lashe zaben zai ba Mista Biden karfin gwiwar fuskantar babban zaben ranar Talata da aka fi sani da Super Tuesday.
Wannan ne zaben fid da gwani na farko da Joe Biden ya lashe tun da aka fara jerin zabukan da za su samar da dan takarar da zai kalubalanci Shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba mai zuwa.
Babu shakka wannan nasara ce da za ta faranta masa har ma da magoya bayansa rai.
Ya dade yana hasashen cewa yana da gagarumin goyon baya a wajen bakaken fatan kasar, musamman na jihar ta South Carolina, kuma ya ce wannan ce allurar da yakin neman zabensa ke bukata domin farfadowa.

Asalin hoton, AFP
Masu zabe a wannan zaben sun taimaka masa gaya, domin da bai lashe zaben ba, da Bernie Sanders ya sha gaban dukkan 'yan takarar, wanda da haka ya faru, to da ya kawo karshen yakin neman zaben Mista Biden.
Bayan wannan zaben, Mista Sanders na da wani dan takarar da zai kalubalance shi a jerin zabukan da za a gudanar ranar Talata - wadanda aka fi sani da zabukan Super Tueday.
A ranar ce jihohin Amurka 14 za su kada kuri'a, matakin da ka iya ba wani dan takara damar shan gaban sauran, kuma ya zama damar tunkarar Shugaban Amurka Donald Trump a zaben shugaban kasa na watan Nuwambar 2020.











