Tara Reade: 'Ina son Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka'

Asalin hoton, Megyn Kelly
Matar da ta tuhumi tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da cin zarafinta shekara 27 da ta gabata, ta nemi da ya janye daga takarar shugaban kasar.
A wata hira da ta yi da 'yar jarida Megyn Kelly, Tara Reade - wadda ta taba aiki a ofishin Mista Biden a lokacin yana dan majalisar dattawan Amurka - ta ce saboda halinsa ba na gari ba ne, bai kamata Mista Biden ya tsaya takara ba.
"Joe Biden ka dai san abin da ya faru tsakaninmu a baya, saboda haka ina kira a gareka da ka yi abin da ya kamata."
Ta kuma ce, "Bai kamata mutum mai hali irin naka ya nemi shugabancin Amurka ba."
Da 'yar jarida Megyn Kelly ta tambaye ta ko tana son ya janye daga takara, sai ta ce:
"Zan so ya janye, amma na san ba zai janye ba. Amma abin da na ke son gani ya faru ke nan."
A watan jiya matar ta kai karar dan takarar wanda zai wakilci jam'iyyar Democrat, duk da cewa babu abin da doka za ta iya yi saboda lokacin shigar da irin wannan karar ya kure.
Wane martani ofishin yakin neman zabe na Biden ya mayar?
Babbar jami'a mai kula da batutuwan sadarwa da hulda da jama'a na ofishin yakin neman zaben MIsta Biden, Kate Bedingfield ta ce hirar da matar ta yi da 'yar jarida Megyn Kelly cike ta ke da "kurakurai."
A cikin sanarwar ta ce, "Ya kamata a gaskata mata a kan irin wannan halin. Ya kuma kamata su iya fitowa fili su bayyana abubuwan da aka yi mu su ba tare da tsoron za a cutar da su ba."
"Amma duk da haka, bai dace mu rika danne gaskiya ba. Kuma batun gaskiya shi ne wadannan bayanan na karya ne domin hujjojin da ake bayar wa sai sauyawa suke yi, wanda ya tabbatar da karya ce kawai".











