Manchester United ta sabunta kwantaragin Matic

Dan wasan tsakiya na Manchester United Nemanja Matic ya sabunta kwantaraginsa da kungiyar na tsawon shekara guda.

Dan wasan mai shekara 31, wanda kwangilarsa ta shekara uku za ta kare karshen wannan kakar, yanzu haka yana tattaunawa da kungiyar kan yadda zai tsawaita zamansa.

Kokarin da Matic ke yi a baya-bayan nan shi ne ya bai wa United kwarin gwiwar sabunta kwantaraginsa zuwa 2021, amma da yiwuwar dan Sabiyan zai iya zama sama da haka a kungiyar.

Matic ya buga wasa 109 ga kungiyar ta Old Trafford tun daga lokacin da ya koma United daga Chelsea kan kudi fan miliyan 40 a 2017.